Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji a jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya tabbatar wa al’ummar mazaɓarsa da cewa bai taɓa goyon bayan sababbin dikokin haraji ba.
Ya ce, “Abin da na ce shi ne, akwai batutuwa da dama da za su zama alheri ga Arewa da Nijeriya. Kuma mu ‘yan Majalisa na yankin Arewa mu yi amfani da rinjayen da muke da shi a Majalisa, mu tsaya daram mu goyi bayan duk wasu ƙudirorin da za su amfani Arewa ta fannonin bunƙasa tattalin arziƙin yankin, waɗanda ke cikin ƙudirorin. Mu kuma cire waɗanda za su cutar da mu, ko mu gyara su a yadda ba za su cutar da mu ba.”
Wannan na ƙunshe ne cikin wata takardar da ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai.
Ya ƙara da cewa, “Kuma mu yi amfani da wannan damar dokar da aka kawo mu bijiro da wasu sabbi da muka tabbatar za su amfani Arewa domin a shigar da su a cikin kundin ƙudirorin. A yayin haka kuma, mu tabbatar da yi wa sauran jihohi da yankunan Nijeriya adalci a tsarin dokar. Amma ra’ayin wasu shi ne a yi watsi da dokar gaba ɗaya.
“A matsayina na mai hawa huɗu a Majalisa, ban taɓa ba, kuma ba zan taɓa goyon bayan duk wata doka ko ƙudurin da zai kawo illa ga mazaɓa ta, jihata Kano ko Arewa da ma Nijeriya ba,” in ji shi.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce, “Amma duk da haka ina bai wa duk waɗanda matsaya ta a kan dokar ya ɓata musu rai da ‘yan’uwana ‘yan Majalisar wakilai, sanatoci, gwamnoninmu, shugabanninmu, sarakunanmu, malamanmu, ‘yan kasuwanmu, ‘yan siyasa, ‘yan bokonmu, ‘yan jaridunmu, mata da matasa da duk jama’armu baki ɗaya haƙuri.”
Kofa ya ƙara da cewa, “Musamman Ubana Jagoran NNPP Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da irin shawarwarin da ya ba ni. A nan zan haɗa da Alƙali Salihu Abubakar na Jamila Zariya da yake jajircewa wajen faɗakarwa. Allah (T) ya yi musu albarka.
“Ina kuma ba d tabbacin cewa zan yi duk abin da zan iya in ga cewa ba a cutar da Arewa ba da kuma ganin an yi wa kowa adalci a Nijeriya a kowane lokaci kamar yadda na saba yi,” cewar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa.