Daga Ibrahim Muhammad
Kwamishinan wasanni da matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nuna rashin gamsuwarsa game da gyaran filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata, Kano.
Kwankwaso a wata tattaunawa da ya yi da ‘yan jarida ya ce, “Babu shakka akwai kurakurai wajen gyara filin wasan, wanda na jawo hankali a kan hakan tun da fari,” in ji shi.
Ya buƙaci Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da ya kafa wani kwamiti da zai binciki yadda aka yi aikin domin gano gaskiya abin da ya faru.
Ya ƙara da cewa wannan gyara da aka yi mataki na farko ne, akwai sauran ayyuka da suka haɗa da gyara wajen gudu na filin da wajen zama na manyan baƙi da ofishin ma’aikata da ke filin wasan.
Kwankwaso ya zargi wasu marasa kishin jihar Kano da yi wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars zagon ƙasa domin a ɗauke ta daga jihar Kano.
Ya jinjina wa Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf bisa nuna kulawa da yake ga ƙungiyar da kuma ci gaban matasan jihar Kano.