Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana aure a matsayin ibada da ke buƙatar yin haƙuri da juna a zamantakewa da mutunta juna da ladabi da biyayya da fahimta da kiyaye dokokin Ubangiji.
Mataimakin sakataren ƙungiyar Ƙwadago na jihar Kano tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu na ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Abbas Ibrahim ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen ɗaurin auren ‘yar gogaggen ɗan jarida Malam Yakub Musa da aka yi a ranar Asabar a unguwar Ƙoƙi a Kano.
Ya ƙara da cewa auren abin farin ciki ne a gare shi, domin shi mahaifin Amarya kusan ƙani ne a gare shi, domin sun zauna da shi a Legas lokacin da ya je yi wa ƙasa hidima, shi kuma yana aiki a wajen Kawunsa wanda a lokacin shi ne shugaban ƙungiyar ‘yan jarida na ƙasa, Sani Zoro. “Mun zauna da Malam Yakub Musa har lokacin da ya samu aiki a jaridar Thursday,” in ji shi.
Kwamared Abbas Ibrahim ya yi nuni da cewa hatta mahaifiyar Amarya zai iya cewa da shi aka auro ta. “Wannan kuma abin alfahari da farin ciki gare ni ƙwarai da gaske da Allah ya sa muka shedi auren ‘ya’yanmu. Ina fatan Allah ya ba da zaman lafiya,” ya jaddada.
Ya ce yana yi wa mahaifin ‘yar su Amarya Sumayya Yakub Musa fatan alkhairi, domin mutum ne shi jajirtacce, tsayayye mai mutunta jama’a. “Irin kyakkyawan halinsa na karrama jama’a ne ya sa daga ko’ina ciki da wajen jihar Kano, musamman ‘yan jarida, ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da ma’aikata ‘yan’uwa da sauran abokan arziƙi suka halarci ɗaurin auren.
A nasa ɓangaren Darakta janar na yaɗa labarai na Gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa da shi ma ya halarci ɗaurin auren da sakataren yaɗa labarai na ofishin mataimakin Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Garba, sun yi fatan Allah ya ba da zaman lafiya, ya sanya albarka ga ma’auratan, sannan sun bayyana Malam Yakub Musa da cewa ɗan’uwa, abokin aiki ne mai mutunta mutane.
Shi ma Uban Amarya, Malam Yakub Musa, wanda gogaggen ɗan jarida ne da ya yi mataimakin na musamman a harkar watsa labarai ga shugabannin ƙasa guda biyu, Malam Umaru Musa ‘Yar’adua da Goodlok Jonathon, wanda kuma yanzu ma’aikaci ne a hukumar sadarwa ta ƙasa da yake zantawa da ‘yan jarida, ya gode wa dukkan waɗanda suka halarci ɗaurin auren na kusa da na nesa da waɗanda suka yi masa addu’a da fatan alheri, kuma kalamansa ba su isa su isar da saƙon godiya ba.
Malam Yakub Musa ya ce abin da kowa yake da buri ya gani ke nan. Ya gode wa Allah da ya ga wannan rana da ya aurar da ‘yarsa, kuma yana fatan Allah ya nuna masa na ragowar ‘yan’uwanta. “Ina cikin farin ciki da abin da na gani, an yi lafiya, an gama lafiya,” ya bayyana..
Ɗimbin jama’a ne daga sassa daban-daban suka halarci ɗaurin auren ciki har da tsofaffin Gwamnonin Zanfara; Sanata AbdulAzeez Yari da Aliyu Shinkafi da suka shaidi ɗaurin aure tsakanin Ango Idris Ibrahim Wakkala da Amaryarsa Sumayya Yakub Musa.