Tue. Apr 1st, 2025

Asibitin Abubakar Imam Ya Jinjina Wa Ma’aikacinsu Da Ya Tsinci Dalolin Amurka Ya Mayar

By Saleh Aliyu Dec 6, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban Asibitin lura da larurar mafitsara na Abubakar Imam da ke jihar Kano, Dakta Amin Imam Yola, ya yaba da kyakkyawan hali da ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan Asibitin ya nuna na gaskiya, inda ya miƙa wasu maƙuɗen dalolin Amurka da ya tsinta ga mai su.

Ya ce, “Muna mutuƙar godiya ga Allah da alfahari da wannan ma’aikacin namu wanda shi ne shugaban ma’aikata na Asibitin, Malam Aminu Umar.

Rahotannin sun ce a lokacin da Malam ke aiki tare da sauran ma’aikata, sai wannan bawan Allah da ake kyautata zaton dubiyar mara lafiya ya zo asibitin ya zubar da kuɗin nasa.

Dakta Amin ya ce daga baya da wanda ya jefar da kuɗaɗen ya dawo yana cigiya, ya yi masa tambayoyin da suka tabbatar da nasa ne, sai ya ɗauko kuɗinsa ya ba shi, har mai kuɗin ya nemi ya yi masa ihsani, amma ya ƙi karɓa. Ya ce wannan hali yabawa ne.

Ya yi godiya ga Allah da wannan halin gaskiya da ma’aikacin nasu Malam Aminu Umar ya nuna duba da yadda yanzu saboda tsananin halin rayuwa ba kowa ne ake da aminci da shi da zai iya haka ba, amma aka sami wannan al’amari na mutum mai kyakkyawan hali da tsoron Allah a cikin Asibitin na Abubakar Imam, kuma babban ma’aikacinsu. “Dole mu yi alfahari da hakan. Shi ma da ya yi wannan kyakkyawan aiki abin alfahari ne a gare shi da dukkan na tare da shi. Dama shi mutum ne da muka san shi mai gaskiya da ƙwazo a wajen aiki,” in ji shi.

Ya yi nuni da cewa ita dama tsintuwa abu ne da ba naka ba, idan ka tsinta, in mai su ya zo sai ka ba shi, kuma ba za ka nemi wani tukuici ba, kuma mai gaskiya da tsoron Allah ne kaɗai zai yi wannan, shi ya sa ko da mai kuɗin ma ya zo ya karɓa ya so ya ba shi tukuici ya ce ba ya buƙata.

Shugaban Asibitin na larurar mafitsara na Abubakar Imam, Dakta Amin Imam Yola, ya bayyana ma’aikacin nasu Malam Aminu Umar da cewa yana daga cikin waɗanda hukumar kula da asibitoci za ta karrama sakamakon gaskiya da amana da ya nuna.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *