Mon. Mar 31st, 2025

Ana Tsare Da Matar Da Ta Kashe Mijinta Da Gatari A Borno

By Saleh Aliyu Jul 21, 2024

An kama wata mata mai suna Lydia Aji mai shekaru 40 da laifin kashe mijinta da gatari a jihar Borno.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yusufu Lawal, wanda ya samu wakilcin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Nahum Kenneth, wadda ake zargin ta samu gardama da mijinta a kan zargin satar akuya da diyarsu mai shekaru 13 mai suna Rachael ta yi.

An ce mijin ya mutu nan take bayan harin, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

Lawal ya ce, “A ranar 4 ga watan Yuli, 2024 wani Bulama Mulikabu, mazan kauyen Kautikari na karamar hukumar Chibok ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda na Chibok cewa, a ranar ne wata mata mai suna Lydia Aji ‘yar shekara 40 da mijinta Aji Makinta, suka yi fadan da ya yi sanadiyar matar Lidiya Aji ta sara wa mijinta gatari a kai, kuma nan take ya mutu.”

Da yake karin haske Lawal ya ce mijin nata da ya rasu ya bukace su da su bar gidansa bayan sun yi sata.

Bincike ya nuna cewa ma’auratan sun samu rashin fahimtar juna a kan ‘yarsu Rachael Aji mai shekara 13 da ta sace akuya ta sayar da ita ga wanda ba a sani ba, mahaifin ya fusata ya ce su bar gidansa.

Har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *