Daga Ibrahim Muhammad
Fitaccen ɗan siyasa a jihar Kano, kuma shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta Jihar, Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Ɗanzago ya kwashe shekaru da dama a harkar siyasa.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar REMASAB ne ya tabbatar da rasuwar Ahmadu Haruna Zago a asibiti.
A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban Hukumar REMASAB.
Jama’a da dama na ci gaba da nuna alhinin rasuwar jigo a siyasar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.