Daga Ibrahim Muhammad
An yaba wa shugaban ƙasa Ahmad Bola Tunubu da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa bai wa jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, wanda ya yi takarar neman majalisar tarayya na Madobi/Kura da Garun Malam a zaɓen 2023, Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso muƙamin babban darakta na kuɗi a hukumar raya kogunan Haɗejia da Jama’are.
Wannan yabo ya fito ne daga ɗaya daga cikin matasan jam’iyyar APC a jihar Kano ɗan ƙaramar hukumar Fagge Dini Falalu.
Ya ce wannan muƙami babbar karramawa ce ga jihar Kano, domin jagoransu Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso mutum ne na mutane mai karamci da taimako, “A koyaushe gida da ofis yana tare da jama’a,” in ji shi.
Ya ce suna da yaƙinin cewa wannan muƙami da aka bai wa jagoransu Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso zai ci gaba da bunƙasa karɓuwar jam’iyyarsu ta APC a jihar Kano don mutum ne da alherinsa da mutunta jama’a, hatta ‘yan jam’iyyu na adawa suna kwatance da yadda yake darajanata mutane da yi musu hidima.
Dini Falalu Fagge ya ce wannan dama da shugaban ƙasa ya bai wa ‘yan Kano a hukumar kula da koguna Haɗejia da Jama’are, Rabi’u Sulaiman Bichii a matsayin Manajan daraktan da jagoransu, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna irin ƙauna da shugaban yake wa jihar Kano. “Wannan matsayi da aka ba su wata dama ce da za su ba da gudunmuwa wajen haɓɓaka noma, musamman noman rani da hakan zai wadata Kano da Arewa da abinci,” ya tabbatar.