Sat. Apr 5th, 2025

An Yaba Wa Ƙoƙarin Babbar Jojin Jihar Kano

By Saleh Aliyu Dec 17, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa zuwan Dije Aboki a matsayin Babbar Jojin jihar Kano, ɓangaren sharia ya samu muhimmin gyara na mutumtaka da cigaba sosai.

Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo a jihar Kano, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a wani taro na ƙungiyar lauyoyi mata a Kano.

Ya yi nuni da cewa aikin tuƙuru da jajircewa a kan gaskiya da kawo gyara a ɓangaren sharia da babbar jojin take yi, shi ya sa sauran ƙungiyoyin mata, musamman na lauyoyi ke duba suna koyi da ita. “Domini na gamsu mata za su iya yin abin da ya kamata a kowane fage duba da irin matakai da babbar jojin jihar Kano take ɗauka na kawo gyara a ɓangaren shari’a, ya jaddada.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce a shugabancin da yake na ƙungiyar lauyoyi na jihar Kano reshen Ungogo ya zo da wasu tsare-tsare guda bakwai da ya sa a gaba domin ya aiwatar da su ɗaya bayan ɗaya, wanda zai zama kamar jagora gare shi domin duk lokacin da ake abu idan akwai manufa da ake so a cimma, sai a ga abubuwa sun zo cikin sauƙi wannan tasa suke ƙoƙarin tallafa wa cigaban ƙungiyar.

Ya ce daga tsare-tsare da suke son cimma sun haɗa da kare haƙƙin ɗan’adam da shi ne manufa gaba ɗaya na uwar ƙungiyarsu, sannan samun haɗaka da fahimta da ƙungiyoyi kamar irin su FIDA da hukumomin jami’an tsaro da kuma tarbiyyantar da ‘yan ƙungiyar kan wajen tsayawa da jajircewa a kan gaskiya da bin doka.

Batista Ahmad Gwadabe ya ƙara da cewa kasancewar ƙungiyar tasu ta lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo ba su da matsuguni na kansu, suna haya ne, daga cikin abin da ya sa a gaba akwai samar da matsuguni mallakar ƙungiyar na dindindin da yardar Allah kafin wa’adin da aka zaɓe su ya ƙare.

Ya bayyana cewa rsssan da ake da su na ƙungiyar lauyoyi ba su da bambanci ‘yan’uwan juna ne, duk suna tafiya a tsari na doka ne kowace jiha tana da dama ta yi rassa sama da ɗaya kamar yadda a Legas suna da reshe sama da huɗu a babban birnin tarayya ma Abuja haka a Kano suke da reshe guda biyu na Kano da na Ungogo, amma duka matsayinsu ɗaya ƙarƙashin uwar ƙungiyar lauyoyin ta ƙasa.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce game da ƙorafi da ake yawan yi a kan lauyoyi da Alƙalai na gabatar da shari’a da ake samun suna karo da juna suna yawan kira ga lauyoyi da Alƙalai a duk wata dama ta haɗuwa da suka samu akan a daina irin wannan irin wannan karon a kotuna daban- daban da hakan ke haifar da matsaloli, musamman wajen ba da umurni. Wannan kotu ta yi na daban wata ma ta yi na daban a kan abu ɗaya.

Ya yi nuni da cewa akwai hukuma da take kula da Alƙalai a matakin jiha da ƙasa gaba ɗaya da ƙungiyar lauyoyyi ta ƙasa suna iya ƙoƙarin su wajen jan hankalin Alƙalai, kuma idan aka samu da wani da gangan wani Alƙali ko Lauya yana yin wani abu da ba daidai ba, suna ɗaukar mataki sosai a kai kama daga na jan kunne har ma dakatarwa.

Da ya juya kan ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar mata lauyoyyi FIDA da mujallarsu da suka wallafa karo na biyu da ya halarci taron shugaban ƙungiyar Lauyoyin reshen Ungogo Batista Ahmad Abubakar ya ce abu ne mai kyau idan aka yi la’akari da irin gudanarwa da suke bayarwa na tsayawa masu ƙaramin ƙarfi da ake cin zarafin su, musamman mata da yara a gaban shari’a don ƙwato haƙƙinsu.

Batista Ahmad Abubakar Gwadabe ya taya sabbin shugabannin ƙungiyar lauyoyi mata na jihar Kano da aka ƙaddamar ƙarƙashin jagorancin Batista Salma Danpappa murna da kuma jan hankalinsu su ƙara ƙwazo da zage damtse a kan irin ayyuka da suke musamman na tsayawa marasa ƙarfi kamar yadda shugabanni da suka gabata suke yi.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *