Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban kamfanin Alyumnah, Alhaji Ali ya bayyana cancantar naɗin da Sarkin Haɗejia Alhaji Abubakar Maje Haruna ya yi wa babban jami’in a hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa, Ahmad Babandede na matsayin Sarkin Rafin Haɗejia.
Alhaji Miko Idris Mai Dubu Darakta a kamfanin Alyumnah, wanda ya yi magana a madadin shugaban kamfanin ya ce su da suka zo baƙi, sun ji daɗi da irin karramawa da girmamawa da al’ummar Haɗejia suka yi musu na naɗa amininsu masoyi, Alhaji Muhammad Babandede a matsayin Sarkin Rafi.
Alhaji Miko Idris Mai Dubu Kureken Sani wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Kumbotso kuma mataimakin shugaban Dattawa ya ce zuwan su naɗin ƙarƙashin jagorancin shugaban kamfanin Alyumah Alhaji Ali sun yin fatan Allah ya sa wa naɗin albarka.
Sun kuma gode wa mai martaba Sarkin Haɗejia da aka yi dogon tunani aka naɗa wannan sarauta ta Sarkin Rafi. Muhammad Babandede wanda mutumin kirki ne, kuma aminin Alhaji Ali Alyumnah.