Tue. Apr 1st, 2025

An Samu Bullar Sabuwar Cuta A Jihar Sakkwato

By Saleh Aliyu Apr 10, 2024

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta tabbatar da bullar wata sabuwar cuta da ba a san ta ba a jihar Sakkwato.

Babban daraktan hukumar, Dakta Jide Idris, ya ce kawo yanzu an gano mutane 164 da ake zargin sun kamu da cutar a unguwanni shida na karamar hukumar Isa da suka hada da: Bargaja (22), Isa ta Arewa (17), Isa ta Kudu (98), Tozai (12), Tsabre (4), da Turba (11). Ya kara da cewa an samu rahoton mutuwar mutane hudu a cikin wadanda suka kamu.

Ya ce ma’aikatar lafiya ta jihar Sakkwato ta sanar da hukumar ne game da rahoton da aka samu na wasu yara da ke dauke da alamomin da suka hada da ciwon ciki, zazzabi, amai da rage kiba. daga karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato ne a ranar 21 ga Maris, 2024.

Ya ce, “Yawancin wadannan matsalolin yara ne masu shekaru 4-13, ciki har da wasu manya.

Marassa lafiyar sun fito ne daga gundumomi da kauyuka daban-daban a cikin LGA.

Dokta Idris ya ce hukumar NCDC ta tura wata tawagar kai daukin gaggawa ta kasa (NRRT) don yin aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar don ci gaba da bincike da nufin shawo kan matsalar.

Ya kara da cewa a baya an samu korafin makamancin haka a shekarar 2023.

A halin yanzu, wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da cutar suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Uthman Dan Fodio (UDUTH) da ke Sakkwato, kuma an sallami daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar.

Ya ce, “Wasu mutane hudu da ake zargin suna dauke da cutar a babban asibitin Isa, yayin da kimanin mutane 130 kuma ke samun kulawa ko dai a cikin cibiyoyin kiwon lafiya na farko (PHC) ko kuma ake kula da su gida a karamar hukumar da abin ya shafa.”

Babban daraktan hukumar ta NCDC ya ce rahoton farko na asibiti da kuma binciken al’amuran ba su fito da asalin cutar ba, wanda hakan ya sa ake bukatar neman wasu dalilai da za su sa a gano asalin cutar ta hanyar gudanar da sabbin gwaje-gwaje.

Ya ci gaba da cewa sakamakon gwajin da aka samu ya nuna cewa akwai gubar dalma mai yawa a cikin jinin wadanda suka kamu da cutar, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da wasu gwaje-gwaje domin gano cutar.

Ya bukaci al’ummar da abin ya shafa da kuma na kusa da su yi taka-tsantsan, tare da kai rahoton duk wanda ya nuna alamun cutar ga cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa da su ko kuma a kira layin NCDC kyauta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *