Mon. Mar 31st, 2025

An Roƙi Kakakin Gwamnan Kano Sanusi Bature Ya Fito Takarar Sanata

By Saleh Aliyu Jan 23, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Tsohon ɗan takarar kansila a mazaɓar Dawanau, Honarabul Abdullahi Ado Mai Kaza, ya bayyana babban daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na gwamnatin Kano, Alhaji Sanusi Bature Dawakain Tofa, a matsayin jigo kuma jajirtacce a yankin Kano ta tsakiya da ma Jihar Kano.

A zantawarsa da manema labarai a Kano, Abdullahi Ado Mai Kaza, ya ce DG Sunusi Bature yayi koyi ne da halin Gwamna Kano Injiya Abba Kabir Yusuf na kishi da tallafawa al’ummar Kano.

“A harka ta ilimi, lafiya, tallafa wa ‘yan jam’iyya da ma duk abin da ya shafi ciyar da ɗan Adam gaba, a cikin shekara 13 da mu ke a tafiyar Kwankwasiyya ba mu da haziƙi jajirtacce irin mai girma Sanusi Bature”

“Ba a daɗe ba a Dawakin Tofa akwai marayun da ba su da yadda za su yi, Sunusi Bature da ya samu labari nan da nan ya saya masu gida ya ba su, haka kuma a satin da ya gabata ma mai girma DG ya tallafa wa makarantar Islamiyya da kuɗi fiye da miliyan ɗaya, ire-iren waɗannan abubuwan alherin ba sa ƙirguwa”, in ji Abdullahi Mai Kaza.

Daga nan ne ya yi kira da kakakin na gwamnan Kano Sunusi Bature da ya fito takararar Majalisar tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, a cewarsa in ya so jaritaccen ɗan majalisa Hon. Injiniya Abdulƙadir Joɓe sai ya fito takarar Sanata a yankin namu mai albarka.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *