Tue. Apr 1st, 2025

An Raba Wa Mata 200 Jari A Fagge, Kano

By Saleh Aliyu Jan 16, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Mata 200 a ƙaramar hukumar Fagge kowacce ta sami jari na ₦50,000 da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sahale a raba musu.

Taron rabon da aka gudanar a harabar sakatariyar ƙaramar hukumar Fagge da shugaban ƙaramar hukumar ya jagoranci bayarwa ya sami halartar sakataren mulki na ƙaramar hukuma Aliyu Tijjani Sanata da zaɓaɓɓun kansuloli sauran masu ruwa da tsaki.

A jawabinsa yayin bikin ƙaddamar da tallafin, shugaban ƙaramar hukumar Hon.Salisu Usman Masu
ya ce, sun tsaya sun yi wannan aiki na rabon tallafi ne da ya jagoranta saboda bin umurnin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaya musu lallai wannan abu ya tafi ƙasa saboda a lokacin yaƙin neman zaɓe ya yi alƙawarin in Allah ya ƙaddara shi ne Gwamna za a taimaki mata da jari.

Ya ce wannan cika alƙawarin ne ɗaya ɗauka wannan kuma ba shi ne na farko ba, an yi na ɗaya da na biyu da na uku. Wannan shi ne na huɗu. “Mun tsaya mu yi aikin ne da kanmu domin mu tabbatar da cewa an yi abin da ya kamata. Allah shi ne shaida, kuma al’umma ma shaida ne duk mazaɓar da muka kirawo akwai jagororanta da kansila da sauran masu ruwa da tsaki a gabansu aka yi komai, kuma abin ya tafi hannun wanda ya kamata,” in ji shi.

Hon. Salisu Masu ya ja hankalin matan da suka amfana da tallafin da cewa kar wani ya zo ya ce zai karɓi wani abu daga wurinta. “Wannan shi ne saƙon Gwamna. Abu ya tafi hannun mata da suka zaɓe mu. Abin da muka yi yana tabbatar wa al’umma da Gwamna ya yi rabon cikin gaskiya da riƙon amana,” ya tabbatar.

Masu ya yi kira ga mata da suka sami wannan tallafi na ₦50,000 su yi amfani da shi yadda ya kamata ‘, “Domin a lokacin Kwankwaso an ba da irin tallafi makamancin wannan, har yanzu a mazaɓa ta akwai mata da za su nuna maka wani abu na tallafi da aka ba su tun wancan lokacin.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *