Wed. Apr 2nd, 2025

An Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Hajiya Malama ‘Yar Kyakke Ɗanbatta

By Saleh Aliyu Feb 15, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An ƙaddamar da littafin tarihin Hajiya Malama ‘Yar Kyakke da marubuci Kamilu Mustapha Buhari ya rubuta a ranar Asabar a harabar Kwalejin koyon harkar jinya da ke Ɗanbatta.

Da yake jawabi a yayin taron, Sarkin Ban Kano, Hakimin Ɗanbatta, Dakta Mansur Mukhtar Adnan ya yaba wa ƙoƙarin marubucin na rubuta littafin sanin kowa ne Hajiya Malama.

‘Yar Kyakke mace ce mai kamar maza a wurin karantar da addinin Musulunci har ta koma ga Allah.

Ya ƙara da cewa wannan littafin yana tunatar da su daga irin gudunmuwar da ta bayar wajen koyar da Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci a garin Ɗanbatta suna farin ciki wannan littafin da aka wallafa na bayanai masu muhimmanci game da yadda ta sadaukar da rayuwar ta wajen koyar da ilimi.

Sarkin Ban ya nuna farin cikinsa da ya zo a matsayin Uban taro sai dai ya ce shi ma ɗa ne gare ta domin aminiyar mahaifiyarsa ce tunda cikinsa ta ce in an haife shi komai dare a kira ta ta yi addu’a, kuma haka aka yi, kuma ta ja shi a jiki fiye da sauran ‘yan’uwansa, don haka rana ce ta farin ciki ta tuna ta.

Shi ma mai sharhi a kan littafin da aka rubuta kan tarihin Malama ‘Yar Kyakke mai shafi 50.

Dakta Kabir Sufi ya bayyana cewa littafin ya yi tsari, kuma wannan tagomashi ne na tunawa da aikin alkhairi da marigayiya Hajiya Malama ‘Yar Kyakke ta gudanar a rayuwarta sai dai ya ba da shawarar kar faɗaɗa littafin a nan gaba.

A nasa ɓangaren mawallafin Littafin, Malam Sa’idu Musbahu Buhari ya ce ya rubuta littafin ne sakamakon Malami a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi Dakta Umar Muhammad, wanda shi ma ɗalibi ne na Hajiya Malama da ya san irin gudunmuwa da ta bayar ya ce masa ya kamata ya yi rubutu a kanta domin babbar Malama ce da ta ba da gudunmuwar ilimi a ƙasar Hausa ta kafa makarantar Ƙur’ani da ta yi shuhura ta yaye manyan mutane.

Marubucin ya ce ya yi amfani da tuntubar ‘yan’uwanta da abokan arziƙi malamai da ɗalibai da maƙwabta da manyan gari wajen tattara tarihinta aka rubuta littafin.

Kuma nan gaba za a ƙara wasu abubuwa daga tarihin nata da irin gudunmuwa da ta bayar a wajen rubuta cigaban littafin.

Shi ma da yake ƙarin bayani ga ‘yan jarida ɗaya daga cikin tattaɓa kunne na Malama ‘Yar Kyakke, Alhaji Abdussalam Aliyu Muhammad Gidan Tsamiya ya ce wannan littafi da aka yi ya nuna muhimmancin mutum ya yi kyakkyawan abu nagari a rayuwa da zai amfanar da al’umma da za a taru ana tunawa da shi.

Ya ce irin ƙoƙari da ta yi na kafa makaranta da jajircewa wajen ba da ilimi da har yanzu alkhairin hakan yake binta. Ya kamata su ma su koyi wannan abu su yi makamancin haka yana da kyau matasa su yi koyi da halayya irin na Hajiya Malama da sauran shugabanni nagari domin a samu rayuwa ta yi kyau da ko bayan ka a tuna ka aka.

Alhaji Abdussalam Aliyu Muhammad Gidan Tsamiya Ɗanbatta ya ce yin littafi na tarhin Hajiya Malama abu ne na farin ciki mara misaltawa, kuma hakan ya ƙara musu ƙaimi su ma a kan su dage da yin wani abu makamancin haka na gina abubuwan alkhairi.

Shi ma Alhaji Uba Kore, wanda ya sami wakilcin ɗan sa Alhaji Almansur Uba Kore sakataren dillalan man fetur na jihar Kano a taron ƙaddamar da littafin na tarihin Hajiya Malama ya ce sun taso su ma sun sami labari na irin gudunmuwa da Malama ‘Yar Kyakke ta bayar a Ɗanbatta sun sami labarin abin da ta yi shi ne mahaifinsa ya turo shi suka zo su ba da gudunmuwa na ƙaddamar da littafin tarihinta.

A yayin ƙaddamar da littafin Alhaji Idris Ahmad ya ƙaddamar a kan N200,000, Alhaji Abdussalam Aliyu a madadin iyalan Gidan Tsamiya sun ƙaddamar a N500,000 cikin waɗanda suka ba da gudunmuwa wajen ƙaddamar da littafin sun haɗa da ƙaramar hukumar Ɗanbatta da Alhaji Uba Kore da ɗan majalisar tarayya na Ɗanbatta da Makoda, Injiniya Hamisu Chidari da sauran mutane da dama a yayin taron an karrama Hajiya Malama da sauran wasu mata da aka zabo bisa irin gudunmawa da suka bayar ga cigaban Ɗanbatta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *