Daga Ibrahim Muhammad
Mai Shari’a ta babban kotun jihar Kano, Hauwa Lawan Umar Minjibir ta muna farin ciki da gode wa Allah bisa zaɓo su da ƙungiyar Minjibir Solidarity Forum ta yi ta karrama su wanda hakan ba dabara ko hikimar su ba ce ba horewa ce ta Ubangiji suna gode masa da wannan karanci da ƙungiyar da take haɗa zumunci da haɗa kan al’ummar Minjibir ta yi musu.
Ta bayyana hakan ne da take zantawa da manema labarai bayan karɓar shaidar karramawar da aka gudanar a Minjibir
Ta ce yadda aka ɗauke su abin misali aka yaba aka nuna domin ‘yan baya ma su yi koyi da shi suna kuma gode wa iyayensu da suka ba su tarbiyya da ilimi har suka sami wannan dama har ake yi musu wannan karramawar.
Ta ƙara da cewa wannan karramawar ya daɗa musu ƙwarin gwiwa da karsashi na yin riƙo da gaskiya da amana.
Da kuma adalci da yin komai bisa aiki da ilmi da bin ɗoron doka, musamman a matsayinta na masu yin hukunci duk abin da ya kama na adalci idan ya zo gabanta za su yi, suna kuma addu’ar Allah ya yi musu jagoranci a kai.
Mai Shari’ar ta babban kotun jihar Kano, Hauwa Lawan Umar Minjibir ta yi kira ga al’ummar Minjibir su dage da yin ilimi da riƙe addini da riƙo da amana da waɗannan abubuwa guda uku babu inda mutum ba zai je a matakin rayuwa ba da yardar Allah.