Mon. Mar 31st, 2025

Al’ummar Doguwa zamu sa a gaba – Abdulrashid Rilwan

By Gazali Haruna Dec 19, 2024 #Doguwar #Kano #Shugaba

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban Karamar Hukumar Doguwa a jihar Kano Abdulrashid Rilwan ya bayyana cewa abin da suka sa a gaba shi ne su tabbatar da hakkin al’ummar Doguwar yana zuwa gare su ana yi musu ayyukan bunkasa kasa.Ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kano. Inda ya yi nuni da cewa akwai ka-lu-bal-e da yawa da suke fuskanta a Doguwa na rashin ayyukan cigaba da ake fama dasu a yankin sakamakon ana turo tarin hakkokinsu na karamar hukumar amma saboda azzalumai sun mallake a matsayin nasu ba sa ayyuka da za su na inganta rayuwar al’umma. Abdulraahid. Rilwan ya ce a tsawon lokacin nan da aka dawo na mulkin Damakwaradiyya a kasar nan, an turo da abubuwa na kason arziki masu dinbin yawa da ya kamata a raya ci gaban yankin, amma wadannan mutane da ke ci da gumin ‘yan yankin ba sa hidimtawa al”umma dasu.Ya ce zuwan su yanzu da yardar Allah gwargwadon hali da iko za su saka danba na kyautata ci gaban yankin tare da bunkasa harkar ilmi da raya kasa, suna kuma da yakinin na sanin zababben Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zai basu dukkan goyon baya da gudunmuwa da zasu tabbatar sun yi aiki na raya kasa da raya ci gaban al’ummar karamar hukumar Doguwa domin duk mutumin da ka taimake shi ka raya shi da al’ummar sa shima akwai kyakkyawan zato zai rama alkhairi da alkhairi.Abdulrashid Rilwan ya ce za su tabbatar dukkan tsare- tsare na kwankwasiyya sun yi aiki da tabbatar da su domin in an bi tsarin al”ummar Doguwa za su ji dadi da farin ciki. Duk da cewa sun zo sun sami tarin matsaloli a karamar hukuma sakamakon Allah ya tara musu wasu da basa kishin al’umma da son ci gaban su sakamakon karamar hukumar ta yi nisa da cikin birni.Ya ce a da al”ummar Doguwa basa samun dama da za su bayyana ra’ayinsu domin a dauki mataki na gaggawa shi yasa mutane marasa kishin da suke kwace musu zabe in sun yi suka sami dama suke danne hakkin al’umma a DoguwaShugaban karamar hukumar Doguwa.Hon Abdulrashid Rilwan ya godewe jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya girmama dan asalin yankin su Umar Haruna Doguwa na bashi dama yake hidimtawa a Gwamnatinsa Hon.Abdulrashid Rilwan Doguwa ya ce wannan dama da ake basu amana ce tasa domin duk dan karamar hukumar Doguwa in dai ba mara daraja ba zaka same shi mai amana da halacci, suna saka alkhairi da alkhairi , duk wanda ya yi musu babban burinsu su saka masa shi yasa suke jinjina ga jagoransu na kasa a siyasa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso domin wannan irin tarbiyya da ya basu suke nunawa a koyaushe

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *