Tue. Apr 1st, 2025

Alhaji Ibrahim Ɗanyaro Zai Dauki Nauyin Karatun Marayu 20

By Saleh Aliyu Feb 18, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Fitaccen ɗan kasuwa kuma shugaban Dattawan kasuwar Muhammad Abubakar Rimi da kasuwar Singa, Alhaji Ibrahim Ɗanyaro, ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatun marayu 20 domin inganta rayuwarsu.

Ya bayyana hakan ne yayin taron walimar sauka da haddar Alƙur’ani na ɗalibai 51, a makarantar Almadina Tahafizul Qur’an da ke garin Dawakin Tofa a ranar Lahadi.

Alhaji Ɗanyaro, ya buƙaci a zaɓo masa ɗalibai marayu 20 a makarantar Almadina waɗanda zai dauki nauyin karatunsu har zuwa matakin sauke littafin Alƙur’ani mai girma.

Ya ƙara da cewa zai bai wa ɗaliban makarantar Almadina da suka yi sauka da haddar Alƙur’ani haɗi da malamansu tallafin gudunmawa ta Naira dubu ɗari biyar-biyar.

Wakilin mai masaukin baƙi a taron, kuma mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ubale Magaji Aliyu, ya taya ɗaliban murna, sannan ya yi alƙawarin bai wa makarantar gudunmawar Naira N100,000 a matsayin sadaka mai gudana ko kuma sadakatun jariya ga mahaifinsa biyu da suka rasu.

Uban taron, mai girma Madakin Madakin Kano, Hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Yusuf Nabahani Cigari, ya hori iyaye da su ƙara himma wurin bai wa ‘ya’yansu tarbiyya Islamiyya, don a samu cigaba da fita daga halin matsin rayuwar da al’umma ke ciki.

Shugaban gudanarwar gamayyar makarantun Almadina Sheikh Auwal Bin Umar, ya ce an samar da makarantar tun sama da shekaru 25 da suka shuɗe, kuma ita ce Islamiyya ɗaya tilo a garin Dawakin Tofa da aka fara karantar da ɗalban ilimi a tsarin lokacin karatu na Yamma duk da cewa akwai tarin makarantun Allo na Yamma da wasu Islamiyyoyi na dare a garin.

Ya gode wa wasu daga cikin waɗanda suka ba da gagarumar gudunmawa don tabbatuwar makarantar da bunƙasar ta kamar sakataren gudanarwar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Malam Sa’idu Musa, wanda ya jagorance ta sama da shekaru goma sha.

Uban gamayyar makarantun Alamadina Malam Saminu Sabi’u ya gode wa iyaye yara, manyan alaramomi da manyan malamai da kuma manyan baƙi maza da mata da suka halarci taron walimar sauka da haddar Alƙur’ani, a harabar makarantar Model Firamare Dawakin Tofa, Kano.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *