
Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa akwai daɗaɗɗiyar kyakkyawar alaƙa da ‘yan’uwantaka da zumunta tun na kaka da kakanni a tsakanin masarautar Haɗejia da ta Kano har yanzu kuma suke a tare.
Alhaji Muhammad Inuwa Babandede Yariman Magajin Rafin Haɗejia ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a lokacin ya halarci bikin naɗin da Sarki Muhammad Sanusi II ya yi wa ɗansa a matsayin Chiroman Kano.
Ya ce wannan zumunci zai ci gaba da wanzuwa da kyautata alaƙa tsakanin masarautun biyu domin nasarar hidimta wa al’umma da kare martabar addinin Musulunci da kuma kyawawan al’adu.
Yariman Magajin Rafin Haɗejia Alhaji Muhammad Inuwa Babandede ya yi kira ga sabon Chiroman na Kano DSP Aminu Sanusi ya yi koyi da irin hali na karamci da mutuntawa da Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi yake da su da son cigaban jama’a.
Yariman Magajin Rafin Haɗejia ya bayyana mutuƙar murnarsa ga naɗin da aka yi wa sabon Chiroman na Kano da yi wa dukkan baƙi da suka halarci naɗin fatan alkahiri da fatan komawa gidajensu lafiya.