Mon. Mar 31st, 2025

‘Yan Ajin Shari’a Na 1999 Sun Kai Wa Kwalejin AKCLIS Ɗaukin Gaggawa

By Saleh Aliyu Dec 29, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Tsofaffin ɗaliban ajin nazarin shari’a na shekara ta 1999 na Kwalejin nazarin shari’a na Aminu Kano AKCLIS sun bayar da gudunmuwar ₦5,000,000 ga uwar ƙungiyar a yayin taron da shugaba Kwalejin ya jagoranta na ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar tsofin ɗaliban na ƙasa.

Ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan aji na 99, Assha Nababa ta ce sun ba da gudunmuwar ne kamar dai yadda malamai da iyaye da masana ke ankarar da su duk da na hidimtawa mahaifiyarsa. “Makarantarka ka ɗauke ta kamar uwa ce a gare ka. A nan ka tashi ka san duk wani abu, ka samu duk abin da kake taƙama da shi,” in ji ta.

Ta ce ba sa alfahari da abin da suka bayar, amma suna gode wa Allah da ya raya su ya yi wa ɗaliban ajinsu albarka. Domin a cikinsu akwai manyan alƙalai, lauyoyi da ‘yan sanda da manyan ma’aikatan gwamnati da malaman makaranta, kuma suna kishin makarantar fiye da tsammani.

Ta ƙara da nuni da cewa akwai makarantu da yawa a jihar Kano, amma suna bai wa wannan makarantar kulawa fiye da kowacce, domin su Musulmi ne, kuma duk ilimi na addini a nan suka same shi, suna kuma alfahari da hakan.

“Ganin makarantar tamu na da buƙatar abubuwa da dama wanda sun lura makarantu da suka zo a bayanta ma sun fi ta samun cigaba, dalilin da ya sa ke nan suke jan hankalin ‘yan ajujuwansu a kan ya kamata su riƙa samar da wani tallafi akai-akai domin ci gaban kwalejin,” ta jaddada.

Assha Nababa ta ce a kwanan nan gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da dokar ta-ɓaci a kan ilimi, da wannan ya kamata duk wani ɗan jihar Kano tsohon ɗalibi ya je makarantarsa ya ga cewa ya ba da gudunmuwarsa domin cigaban ilimi su, kuma a matsayinsu na AKCLIS ajin nazarin sharia aji na 1999 sun ba da gudunmuwa ta N5,000,000 domin cigaban Kwalejin da haɓɓaka koyo da koyarwa.

Hajiya Assha Nababa ta ja hankalin shugabannin ƙungiyar da aka zaɓa su mai da hankali su jajirce wajen ganin sun sama wa makarantar cigaba, domin suna da matsaloli da yawa, ko ajujuwa ba sa isar ɗalibai, inda ake yi wa ɗalibai lakca babu yanayi mai kyau. “Don haka shugabannin ƙungiya da ɗalibai na makarantar tunda ta haifar da manyan mutane a sassa daban-daban su taimaka mata,” ta bayyana.

Ita ma A’isha Salisu Muhammad, wacce ita ce Ma’ajin ƙungiyar ta ‘yan ajin shari’a na 1999 na Kwalejin nazarin shari’ar na Aminu Kano ta ce, duk abin da suka zama ita ce zula. “Mun sami tarbiyya daga malamanmu mun haɗa kanmu. Kuma muna bai wa makarantar tallafi daidai gwargwado. Duk shekara muna shigowa muna tallafawa, kama daga kujeru, kayan karatu, da duk wani abu da ake buƙata,” ta ƙarƙare.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *