
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya EFCC ta ce makarantar ‘AMERICAN INTERNATIONAL SCHOOL da ke Abuja, ta tura Dala 760,910.84 zuwa cikin asusun hukumar.
Kuɗin wani ɓangare na Dala 845,852 da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya biya a makarantar don karatun ‘ya’yansa biyar da za su yi a makarantar nan gaba, kamar BBC ta ruwaito.
Mai magana da yawun hukumar ta EFFC, Wale Oyewale, ya shaida wa BBC, cewa tun da farko makarantar ta rubuta wa hukumar takarda, cewa za ta mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnati kasancewar hukuma na bincike a kan lamarin.
Daga nan ne kuma EFCC ta aike wa makarantar asusun da ta sanya kuɗin a ciki, kamar yadda mista Oyewale ya bayyana .
EFCC dai ta yi zargin cewa tsohon gwamnan na Kogi da cire kuɗin daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake jan ragamar jihar, inda ya kai su kasuwar musayar kuɗi, don biyan kuɗin karatun ‘ya’yansa har zuwa wasu shekaru masu zuwa a nan gaba.
A ranar 18 ga watan Afrilu ne dai hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar kogi a lokacin da yake mulkin jihar.
Bayan hakan ne kuma hukumar shige da fice ta Nijeriya ta fitar da wata sanarwa tana umartar jami’an hukumar da su kama shi a duk inda suka gan shi a faɗin ƙasar.
Hukumar shige da ficen ta kuma aike da kofin sanarwar ga rundunar ‘yan sandan ƙasar da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya.
Haka shi ma babban lauyan gwamnatin ƙasar, kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya buƙaci tsohon gwamnan na Kogi ya miƙa kansa ga hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasar.
Yahaya Bello – wanda shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi na huɗu – ya mulki jihar wadda ke tsakiyar Nijeriya, har tsawon wa’adi biyu, daga shekarar 2016 zuwa 2024.
Tsohon gwamnan mai shekara 46, ya kuma tsaya takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023 da ya gabata.