
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hon Bello Jadda Sharifai mataimakin na musamman ga Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a kasuwar waya na titin Beirut, wanda kuma ɗan takarar shugabancin ƙungiyar ‘yan kasuwar ne, ya ce takarar da yake ta amsa kiran da matasa da iyaye ne suka yi masa na ya fito bisa la’akari da gudunmuwa da yake bayarwa ga ci gaban sana’ar.
Ya ce sama da shekaru 20 suke a cikin harkar saye da sayarwa da gyaran wayar
sun san matsalolin harka da alfanunta da su aka soma ƙyanƙyashe sana’ar tun farkon zuwan waya tun daga bakin Post Office da Farm Centre da titin Beirut duk ana damawa da su.
Hon. Bello Jadda Sharifai ya ƙara da cewa yana da manufofi na alhairi da yawa a kan wannan takara tasa musamman na son su ciyar da kasuwar waya ta titin Beirut gaba fiye da yadda take a yanzu.
Ya yi nuni da cewa kasuwar waya ta titin Beirut ita ce kasuwa guda ɗaya da ake zuwa daga ƙasashen yammacin Afirka ake sayen wayoyi a cikinta da kuma take da tarin shagunan kamfanonin waya, amma duk da wannan matsayi nata abin takaici babu wani mutum tilo ɗan asalin jihar Kano a kasuwar da sauran kasuwanni na waya da ke Kano da yake da ‘dealership’.
Ya ce akwai abokan zaman su da ba ‘yan asalin jihar Kano ba, su suke ta rakawa domin sune ke da ‘dealership’. Don haka suke so da izinin Allah da taimakon gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf da taimakon ofishinsa na mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano a kasuwar titin Beirut, za su yi mai yiwuwa wajen sama wa ‘yan asalin jihar Kano wannan dama ta ‘dealership’ ɗin.
Hon. Bello Jaddah Sharifai ya ce idan aka sami wannan damar ta ‘dealership’ ga ɗan asalin jihar Kano, yadda ake gasar harkar kasuwanci, to hakan zai taimaka wajen samun sauƙin farashin waya saboda kowane ‘dealership’ zai so ya yi sauƙi domin a sayi kaya a wajensa, saɓanin a ce mutum ɗaya ne yake da ita. Shi ne zai yi farashin da ya ga dama.
Sai dai ya ce wannan kuma ba yana nufin suna ƙoƙarin yin haka ne domin tauye wani domin ba ɗan asalin jihar Kano ba ne, amma suna so ne al’umma su sami sauƙi, domin yadda waya ta zama abokiyar rayuwa a kowane yanayi idan ya zama akwai ‘yan asalin Kano a harkar a kasuwar Beirut, wacce ta zama wata babbar cibiya ta kasuwancin waya a Nijeriya da Afirka, za su sami dama wajen inganta harkar.
Sharifai ya ce yanzu kusan harka a rayuwa a komai ya juya ta fasahar zamani, kuma a kasuwar waya ta kan titin Bairut kaso 9 na masu harkar waya duk matasa ne, cikin su akwai masu ƙarfi da tsaka-tsaki da ma na can ƙasa. “A ƙarƙashin ofishina na mataimakin Gwamna na musamman kan kasuwar waya ta titin Beirut ma akwai shiri da muke tsara wa matasa da za a bai wa masu harkar waya ta fannoni daban-daban kama daga gyaran waya da sayar da kayan waya da masu kwamfuta tallafi,” ya jaddada.
Ya ce a tsarin za a soma daga kasuwar Beirut, sannan a yi a dukkan kasuwannin Kano a tantance su a ba su jari a horar da masu gyaran waya a ba su kayan gyara don su ma su horas da wasu. Sannan masu harka da na’ura mai ƙwaƙwalwa wajen sabunta manhajar waya su ma za a bai wa matasa horo a kai.
Hon. Bello Jadda Sharifai ya yi kira ga ‘yan kasuwar waya na titin Beirut da cewa suna mutuƙar buƙatar haɗin kai da goyon bayansu a kan wannan takara da yake na shugabancin kungiyar kasuwar domin kai wa ga nasara da zai kawo tsare-tsare da nufin ƙara bunƙasa cigaban kasuwar.