Tue. Apr 1st, 2025

Abin Da Ya Sa Na Amsa Kiran Neman Takarar Shugabancin Ƙungiyar Masu Sayar Da Magungunan Ƙwari Ta Kano -Alhaji Abdulƙadir Gambo

By Saleh Aliyu Feb 7, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Alhaji Abdulƙadir Gambo Ɗankoli, ɗaya daga cikin ‘yan takara da ke neman shugabancin ƙungiyar masu sayar da maganin ƙwari ta jihar Kano da aka fi sani da Kano State Agro Chemicals Dealers Association, ya ce, ya amsa kiran ‘yan ƙungiyar ne na tsayawa takara da niyya ko burin ya ga ya taimaka wajen cigaba da bunƙasa sana’arsu.

Alhaji Abdulƙadir Gambo Ɗankoli, wanda shi ne shugaban kamfanin Abdul Adam Venture, kuma shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na makarantar Sakandire ta Gwammaja Two ‘yan aji na 1990, kuma shugaban ƙungiyar cigaban matasa na Lamma shi ne ya bayyana haka da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya bayyana cewa sana’arsu ta sayar da maganin ta daɗe tana fuskantar ƙalubale tsawon lokaci, musamman na rashin ‘yanci da yawan musgunawa da ake musu daga wasu jami’an tsaro, koyaushe suka sayar da kaya ga abokan cinikansu da suka sayi kaya suka fita da su daga kasuwa, ko kuma idan suka tura yaransu da maganin ƙwarin za su kai tashar mota sai jami’an tsaro su tare su karɓi kuɗi a wajensu alhali ba kayan laifi suke sayarwa ba yana da nufin kawo ƙarshen irin wannan abu da ake musu.

Alhaji Abdulƙadir ya yi nuni da cewa shi ne ya taɓa bayar da shawara ga magabatansu da suke riƙe da shugabancin ƙungiyar sama da shekaru 30 da ba su wuce mutum 10 ba da daɗi, babu daɗi suna yi mata hidima saboda ba a taɓa yin zaɓen shugabanni ba tun kafa ta, ya ba da shawarar a zo a yi mata tsarin shugabanci na zaɓe da karɓa-karɓa na shugabanci aka amince da haka aka tara jama’a a wani taro da aka taɓa yi a sansanin ‘yan yawon buɗe ido aka fitar da shugabanci na riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bello Waziri da mataimakansa da Sakatare da Ma’aji da jami’in hulɗa da jama’a ake ta tafiya har aka zo aka fitar da kwamitin dattawan ƙarƙashin shugabancin Alhaji Bala Larabawa da su ake zama taro da ake gudanar na ƙungiyar.

Ya ce a ƙarƙashin shugabancin na riƙo an sami nasarori masu tarin yawa da suka haɗa da yi wa ƙungiyar rijista ta CAC, aka samar mata Lauya da buɗe dandali a manhajar WhatsApp da ake tuntuɓar juna a kan lokaci a kan abin da ya taso da ya shafi cigaban ƙungiya ko akasin haka.

Kwamitin riƙon da yanzu kusan shekaru biyu ke nan yake gudanar shugabanci har zuwa yanzu da ake shirin gudanar da zaɓe don samar da zaɓaɓɓun shugabannin da za su cigaba da gudanar da ƙungiyar.

Alhaji Abdulƙadir Gambo Ɗankoli ya ce da farko ba shi da wani nufi na shiga neman takara shugabancin ƙungiyar duba da yadda shi ma nauye-nauye da suke a kansa, amma sai al’umma suka matsa lallai ya fito wataƙila akwai abin da suka hanga. Don haka ya bai wa Allah zaɓi ya amsa ya fito wannan takara ta neman zama shugaban ƙungiyar na masu sayar da magungunan ƙwari ta Kano.

Ya ƙara da cewa suna faɗar irin ƙudurori da tsare-tsaren da za su zo da su da suka ƙunshi haɗa hannu da masu sana’ar maganin ƙwarin don su kai ga nasara ta cigaba da bunƙasa sana’arsu da maganin wasu matsaloli da suke fuskanta a ɓangarori da dama da suka ci masu tuwo a ƙwarya.

Alhaji Abdulƙadir Gambo Ɗankoli ya ce, akwai kamfanoni da ake da su na magungunan ƙwari sama da 30 a ƙasar nan, kuma jihar Kano ce take tallata kayan su, sune abokan kasuwancinsu da tura su duk inda za su je a ciki da wajen ƙasar nan, amma suna fuskantar matsaloli tsakaninsu da kamfanonin.

Wannan na ɗaya daga cikin abin da suke so su kawo gyara a kai da za a kyautata alaƙa tsakaninsu ta nemawa ‘yan ƙungiyar haƙƙoƙinsu, idan ya zama shugaban ƙungiyar da yardar Allah.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *