
Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Rauda da ke Rangaza a ƙaramar hukumar Ungogo a jihar Kano da Daraktan Makarantar Rauda Imam Muhammad Yakub ya kafa da cewa tana ba da gudunmawa a inganta harkar lafiya a cikin al’umma.
Malam Isa Safiyanu Umar mai kula da hada-hadar kudi na Kwalejin kimiyyar lafiya da Fasaha ta Rauda ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a madadin darakta janar na makarantun Rauda Imam Muhammad Yakub.
Ya ce daga manufar kafa makarantar shi ne don taimakawa al’umma don matso da tarbiyyar yara kusa da kuma gina su samun horo a kan ilimin kula da lafiya da sana’a.
Ya yi nuna cewa Daraktan kwalejin Muhammad Yakubu ya lura da muhimmancin horar da matasa harkar kula da lafiya, sai ya samar da Kwalejin aka soma yin kwas a matsayin matakin sanin makama.
“Ana ba da horo kan abin da ya shafi harkar lafiya. Ana son dalibi ya sami horo a nan, sai ya nemi gurbi a wata makaranta ta lafiya ya ci gaba wannan kan sa darasin ya zame masa da sauki,” in ji shi.
Malam Isa Safiyanu Umar ya ce a haka sun kai matakin da ake alfahari da dalibai da suka sami horo a fannin lafiya a Kwalejin, daga wannan mataki ne suka sami rijista da ma’aikatar lafiya, sannan suka yi haɗaka da wata makaranta a Saminaka suna ba da horo a kan harkar lafiya da a halin yanzu sun kai gaba ta karshe suna zaman cikakkiyar Kwalejin koyar da kimiyyar lafiya da fasaha nan gaba ma suna a kan matakin da za a sahale musu yin darussa a kan lafiyar al’umma da fannin magunguna da sauran darussa.
Ya kara da cewa tunda fari sun soma horar da dalibai ne guda 15 a fannin lafiya, amma cikin gajeren lokaci dalibai sun kai 80 har yanzu ta kai duk lokacin da suka bude dauka dalibai karuwa suke. Yanzu suna da dalibai 115 maza da mata da malamai 15 na dindindin da kuma wadanda ba na dindindin ba.
Ya kara da cewa yanzu akwai darussa da suke yi sun kai 10. Amma sun fi bai wa guda uku daga ciki muhimmanci. “Yanzu muna yin Community Health, Medical Laboratory da Public Health da sauransu.
Ya ce yanzu al’umma sun fahimta sosai suna kawo ‘ya’yansu suna ba su goyon baya yanzu tsakanin su da iyayen yara sai sambarka da godiya musamman idan yaro ya yi wani abin bajinta.
Ya ce a fannin lafiya ana so mutum ya zama natsattse mai tarbiyya wajen kula da mara lafiya ta kiyaye al’ada da addininsa. “Muna kokari ganin dalibai sun dabbaka hakan duk inda suka sami kansu,” ya tabbatar.
A nasa bangaren rajistara na Kwalejin kimiyyar lafiya da fasaha na Rauda, Abubakar Salihu ya bayyana cewa suna yin tsare-tsaren daukar yara da suka cancanta domin sai wanda yake da karatu na darussa a bangaren Kimiyya da Lissafi ya cika ka’ida shi ake bai wa dama ya yi karatu a Kwalejin.