Tue. Apr 1st, 2025

Abba Kabir Yusuf Ya Bai Wa Ilimi Muhimmanci -Doguwa

By Saleh Aliyu Dec 10, 2024

An bayyana Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa babu wani abu da ya fiifita a gabansa da ya wuce harkar bunƙasa cigaban ilimi ta bijiro da tsare, tsare na cigaban ilimi, amma sai an yi haƙuri abubuwa za su tafi yadda ake so sakamakon irin matsalolin da suka zo suka samu a harkar ilimi.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Hon. Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yayin taron walima da ƙungiyar shugabannin makarantun Sakandire suka shiryawa sabon sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi na jihar Kano, Kwamared Bashir Baffa Muhammad.

Ya ce zuwan su gwamnati sun tarar da harkar ilmi a wani mawuyacin hali wataƙila da dama-dama a makarantun Sakandire, amma a makarantun Firamare wasu wuraren idan ka je duk mai son cigaban ilimi sai ya zubar da hawaye.

Ya ƙara da cewa hatta kuɗin jarabawar makarantun Arabiyya na ‘yan shekarar 2021 da 22 da 23 ba a biya ba, tana riƙe a wajen Hukuma. “Idan akwai yaro da ya yi jarabawar ƙarshe ta makarantar Arabiyya a Kano, wani da ya yi a jihar Jigawa, shi na Jigawa yana mataki na biyu ko na uku a Jami’a, amma na Kano na gida bai ma karɓi sakamakon jarabawar ba sai zuwan Abba aka biya,” in shi.

Ya ce sun samu makarantun Firamare a Kano ta Arewa guda 300, gaba ɗayansu Malami ɗaya ne a kowaccensu. “Abubuwa na takaici da jin haushi da suka gani lokacin da ya zo yana zagaye a Kwalejin Fasaha ta ƙofar Nasarawa ɗakin gwaje-gwaje na Kwalejin wani ya mayar banɗakinsa. Wannan na daga irin lalacewar da muka sami ilimi a ciki,” in ji shi.

Doguwa ya ce da su da malaman makarantu da Gwamnan Kano aiki ne me nauyi na a kansu yadda za su gyara ilimin jihar Kano, aikin yana da wahala musamman ga shugabannin makarantu. “Duk wanda yake makarantar kwana shaida ne akwai lokacin da a baya shugabannin makarantun ne ke haɗa kuɗi su ciyar da ɗaliban, amma yanzu wannan ya kau, abubuwa na gyarawa,” ya jaddada.

Ya ce yanzu an wadata makarantu da kayan aiki, kuma ana tsare-tsare na bai wa malamai guda 1000 bashi, yanzu akwai kayan dakin gwaje gwaje guda 300 da Gwamna ya samar da za a raba makarantu duk abin da ake ana yi ne domin gyara ilimi a jihar Kano.

Ya ja hankalin shugabannin makarantu da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na sane da halin da suke ciki na kuɗaɗen gudanarwa na makarantunsu, kuma komai ya kusa kawo ƙarshe. “Muna godiya ga Allah bisa matakai da ake ɗauka hakan tasa a bana jihar Kano ta zama ta biyu a cin jarabawar da ɗalibai suka yi.”

Shi ma a nasa jawabin, Alhaji Bashir Baffa Muhammad da aka shirya walimar domin taya shi murnar ya ce yana neman a taya shi da addu’ar Allah ya sa ya sami damar taimaka wa cigaban ilimi a Kano.

Kwamared Baffa Muhammad ya ce abin da yake soma a sani Allah ya haɗa shi da wadanda suka so ya koyi aiki, shi kansa Kwamishina ya same shi aikin da babban sakataren dindindin yake kusan shi yake koya masa, kuma ya zo ya sami Kwamishina da ya fi shi ƙaunar ya ga cigaban ilimi.

Sakataren na dindindin Bashir Baffa Muhammad ya ce abin da ya fahimta da zama da Kwamishina Haruna Doguwa shi ne gaba ɗaya ƙudirin da Gwamna yake so ya gudanar a jihar Kano shi ma ya hau kai, kuma shi ma yana sa shi a tafarkin al’umma da ta taru don ta ya shi murna ya nuna Gwamnati ta na kan tafarki.

Bayanin da Gwamnan Kano Abba Kabir yake na a dafa wa ilimi, muhimman mutane da dama da ya ga irin fuskokinsu ya nuna ana amsa kiran gwamnati na dafawa ilimi.

Shi ma a jawabinsa ga ‘yan jarida Malam Abdulkarim Ibrahim Abubakar shugaban kwalejin nazarin Alƙur’ni na Abdullahi Bayero ɗaya daga waɗanda suka shirya walimar, ya ce sun shirya ne domin taya sabon sakataren na dindindin na ma’aikatar ilimi Bashir Baffa Muhammad murna a matsayinsa na ɗaya daga cikinsu.

Malam Abdulkarim Ibrahim ya ce Bashir Baffa Muhammad mutum ne shi na mutane mai son jama’a da karamci da alheri da sauƙin kai duk da wannan babban muƙami da ya samu kullum yana nuna kansa a matsayin daidai suke da shi, dan haka za su ba shi haɗin kai da goyon baya don cimma nasara.

Da take zantawa da ‘yan jarida, ita ma shugabar ƙungiyar shugabannin makarantun Sakandire (ANCOPSS) ta jihar Kano, Hajiya Uwansu Ahmed Balarabe ta bayyana sabon sakataren dindindin ɗin na ma’aikatar ilimi da cewa mutum ne da ya ba da gagarumar gudunmuwa a kan ilimi tun daga matakin malamin makaranta, ya yi shugaban makaranta da sauran muƙamai a ɓangarori na cigaban ilimi. “Muna da yaƙinin zai yi yi aiki tuƙuru wajen cimma nasara manufofin bunƙasa ilimi da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ba shi muhimmanci,” ta jaddada.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *