Tue. Apr 1st, 2025

Abba Kabir Yusuf Ɗan Amana Ne -Hon. Bombay Gama

By Saleh Aliyu Jan 7, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Jigo a jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Muhammad Adamu Bombay Gama, ya bayyana cikar Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf shekaru 62 a duniya a mstsayin alheri bisa dama da ya ba shi ta hidimtawa al’ummar jihar Kano.

Ya ce suna mutuƙar farin ciki da ƙarin shekaru da Abba Kabir Yusuf ya yi, domin mutum ne fasihi jajirtacce mai biyayya ga na gaba da shi, wanda a shekaru 62 ɗin nan saboda amana da biyayyarsa ta sama da shekaru 40 yana tare da jagoransu Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a aiki da hidima da siyasa, ba a taɓa samun wata matsala a tsakaninsu ba.

Hon. Muhammad Adamu Bomboy ya ƙara da nuni da cewa wannan ya nuna Gwamna Abba Kabir Yusuf mutum ne ɗan amana mai gaskiya da ya san karamci da biyayya.

Bombay ya ce suna daɗa godiya ga Allah da ya ba su injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano da a cikin kusan shekaru biyu da soma mulkinsa yana hidimtawa mutane ta yi musu ayyuka managarta na ci gaban da bunƙasa cigaban jihar Kano a fannoni da dama.

Hon. Muhammad Adamu ya yi addu’ar fatan alheri da ƙarin shekaru masu yawa da albarka ga Gwamna Abba Kabir Yusuf don ya samu dama ta cigaba da hidimtawa al’ummar Kano.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *