Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban ƙungiyar TOKAN (Trycles Operators Association Kano State), Alhaji Rayyan Yusuf ya bayyana haɗe ƙungiyoyin mamallaka da matuƙa baburan A Daidaita Sahu domin yin magana da murya ɗaya da cewa abu ne mai kyau da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Ya yi nuni da cewa a baya ma an taɓa makamancin
hakan, kuma su masu bai wa manufofin gwamnati goyon baya ne. “Wannan abu ne mai kyau da muke murna da shi don zai taimaka wajen inganta abin da muke domin amfanin al’umma”, in ji shi.
Alhaji Rayyan ya yi nuni da cewa samar da wannan ƙungiya da ƙungiyoyin A Daidaita Sahu za su riƙa magana da yawun ɗaya ba yana nufin an rusa ƙungiyoyin ba ne, kowace ƙungiya tana nan a matsayinta, yanzu dai an yi musu shugabanci ne kamar a ƙarƙashin lema ɗaya da kowace ƙungiya take ciki. “Sannan idan gwamnati za ta sauko da wani abu ga ƙungiyoyin ‘yan A Daidaita Sahu ko wani abu da za a yi za ta kirawo shugabancin VOTORA ta faɗi abin da za a yi.
Ya ba da misali da cewa kamar a baya ne, TOKAN ƙungiyoyi ne guda bakwai aka haɗe su aka ba da sakataren daga ɓangaren gwmnati aka yarda sun zama ɗaya. “Sannan aka yi zaɓe shugabanmu na farko shi ne Sani Sa’idu Ɗankoli, ni kuma ya yi masa mataimaki, ya yi wa’adi biyu ya sauka, ni kuma na zama shugabanta na yanzu,” ya jaddada.
Alhaji Rayyan Yusuf ya ce don haka wannan tsari da aka yi na samar musu da murya ɗaya a ƙarƙashin shugabancin riko na Kwamred Nazifi BK. Gidan Kuɗi suna fata in Allah ya yarda zai zame musu alheri gaba ɗaya tun daga kan su shugabannin ƙungiyoyin A Daidaita Sahu da masu jan baburan da mamallaka.
Ya yi kira ga sabbin shugabannin na VOTODA a kan yin riƙo da gaskiya da adalci, hakan zai sa mambobi su gamsu da irin manufofi da ake so a cimma da zai kyautata harkokinsu.
Shugaban ƙungiyar ta TOKAN, Alhaji Rayyan Yusuf ya ce su a ƙungiyance a shirye suke su ba da gudunmuwa ga gwamnati ko da na dawo da karɓar haraji mai sauƙi ne, daga mambobinsu domin zai riƙa taimaka mata wajen aikace-aikace da al’umma ke cin gajiyarsu na gyaran hanyoyi da sanya fitilu don an ce su ma su zo su bayar da haraji ba laifi ba ne.
Alhaji Rayyan Yusuf ya yi kira ga ‘yan ƙungiyoyin su na baburan A Daidaita Sahu da ma sauran jama’a su zama masu kiyaye doka, su kuma a ƙungiyance za su bai wa gwamnatin haɗin kai da goyon baya a kowane lokaci domin a cimma nasarar abin da ake nema.