Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban PDP ‘Iyali Ɗaya’ na ƙasa, Ambasada Abdurrahman Mansur Salga Mai Nasara’ Dala, ya karrama sabbin zaɓaɓɓun shugabannin jam’iyyar PDP na ƙaramar Hukumar Dala da na mazaɓun yankin 12 bisa nasarar da suka samu a zaɓukan da suka gabata.
Taron, wanda aka gudanar da shi a ɗakin taro na Mambayya House da Kano, ya samu halartar shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, Hon. Yusuf Ado Kibiya, wanda mataimakin na shiryar Kano ta Kudu, Alhaji Abubakar Magaji Ɗan Bala ya wakilta.
A jawabinsa a taron, Alhaji Ɗan Bala ya yaba wa ƙoƙarin Ambasada Mai Nasara wajen shirya wannan walima da karramawa a ƙoƙarinsa na haɗa kan ‘yan jam’iyyar PDP.
A jawabinsa, Ambasada Hon. Abdurrahman Mansur Salga ya ce, ya haɗa taron walima da karramawar ne ga shugabannin jam’iyyar PDP, domin bai kamata a ce an gama zaɓe, kuma a yi shiru ba, sai kuma lokacin da ake da buƙatar takara sannan a zo nemi al’umma. “Wannan ba shi ne a gabanmu ba. Domin idan kana yin jam’iyyar PDP da gaske, ya kamata ka riƙa bibiyar al’umma ka ji halin da suke a rayuwa,” in ji shi.
Ambasada Salga ya ce ba wani abu ne ya fito da su a cikin tafiyar jam’iyyar PDP ba, sai domin kishin cigaban al’umma. “Allah ya sani ganin irin halin da ƙasar nan take ciki muka fito domin ba da gudunmuwa a cikin rayuwar al’umma. Ba kawai kana da dukiya ka tsaya daga kai sai ‘yan’uwa, sai ‘ya’yanka ba. Ka duba halin da al’umma ke ciki ka taimaka musu,” ya jaddada.
Ambasada Hon. Abdurrahman ya ce taron na yi wa waɗanda suka yi nasarar zama shugabannin jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Dala walima ne da kuma tabbatar da cewa PDP har yanzu jam’iyya ce mai tasiri sosai da take karɓuwa ba kamar yadda masu iƙirari ke cewa ta mutu ba.
Ya ce a matsayinsu na matasa masu kishi za su tabbatar da cewa tafiyar nan da suke nan gaba PDP za ta karɓi mulki a Nigeriya a kowane mataki a zaɓen 2027.
“Ba za mu riƙe hannunmu a PDP ba a halin da ƙasar nan ke ciki ba a halin yanzu. Idan jagororinmu sun yi sanyi, to su bar wa matasa mu za mu iya aikin,” in ji shi.
Ambasada Abdurrahman Mansur Salga ya ce, “PDP iyali daya” yanzu ta amsa sunan ta, kuma za a cigaba da haɗa kan ‘yan jam’iyya babu maganar wani rarrabuwar kai.
Ya ce, “A halin da ake ciki kowa yana ji a jikinsa, babu wanda zai so ya yi wata jam’iyya idan ba PDP ba. Duk da cewa jam’iyya mai mulki da take gallaza wa al’ummar ƙasa suna shirya wani abu domin tabbata a kan mulki ko al’umma ba sa so, amma mu da Allah suka dogara, kuma da yardarsa PDP za ta yi nasara a zaɓen da ke tafe.”