Tue. Apr 1st, 2025

A Daina Tsangwamar Matasa Masu Shaye-Shaye -Mustapha Ɗandinshe

By Saleh Aliyu Feb 20, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa duk matashin da da ya jefa kansa cikin harkar ta’ammali da shan miyagun ƙwayoyi, wannan abun a tausaya masa ne ma a cikin al’umma. “Bai kamata ya zama kyara, tsangwama ko misgunawa ba.”

Wani Matashi a Ɗandinshe da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge, Mustaph Isa ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya yi nuni da cewa abin da ya kamata a yi shi ne jawo irin waɗannan matasa a jiki a riƙa nuna musu illar yin shanye-shaye, a kuma bi su da addu’o’i na neman shiriya. Ba wai a kira jami’an tsaro su riƙa kama su ba. Idan ba su da kuɗin da za su biya a sake su, sai a tura su kotu.

Ya yi zargin cewa wani lokacin wasu ma ƙazafi ake masu don a tsoratasu a ce musu duk abin da Alƙali ya tambaye su a kan abun da aka ce ana zargin, su amsa saboda samun rangwame.

Ya ce, “Kuma da zarar sun amsa a gaban Alƙali sai a yi musu tara, idan babu halin biya sai a tura su gidan gyaran hali. Idan ba a yi dace ba, su haɗu da mugayen abokan zama can. Idan sun fito sai ka ga abin da suke yi ma ya fi na baya. Sai su addabi mutanen unguwarasu da sace-sace da rigingimu kala-kala, alhalin mutanen unguwar sune silar ƙara tunzura su.”

Don haka matashin
Mustapha Isah Ɗandinshe ya ce a fahimtarsa yana ganin ba wannan hanyar ya kamata a bi ba don kawar da matsalar shaye-shaye daga cikin unguwanni.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *