Daga Ibrahim Muhammad
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Barista Muhammad Bello Shehu, ya bayyana cewa su kan su a cikin ‘yan Majalisun Tarayya akwai ‘yan Kudu da ba sa goyon bayan wannan doka ta harajin VAT.
Ya yi nuni da cewa ba a ce kar a yi wannan doka ba, “Amma maganar da muke ita ce, na farko mene ne na yin sauri a dokar? Ita dai doka musamman irin wannan da za ta taɓa rayuwar mutane wajibi ne a bi ta daki-daki kafin a kai ga ƙaddamar da ita a ce ta zama doka,” in ji shi.
Hon. Fagge ya ba da misali da cewa, “A halin da ake ciki game da dokar, mafi yawansu ‘yan majalisu ma ba su fahimci me dokar ta ƙunsa ba. Ɗan majalisar da bai fahimta ba, ta yaya zai koma gida ya fahimtar da mutanensa?”
Ya ce abu ne da yake buƙatar lokaci a fahimci dokar, sanan su koma gida su fahimtar da mutane game da halin da ake ciki. Amma dai dokar nan ba su ga inda za ta iya zame wa Nijeriya, ba ma Arewacin ƙasar nan ba alheri ba.
Hon. Muhammad Bello Shehu ya ce, “Misali akwai sashi a dokar da yake maganar ‘harmonising tax’ wanda ya shafi tattara kuɗaɗe da ake bai wa TETFUND da harkar fasaha da na sadarwa duk a kuɗaɗen harajin ake ɗan gutsurar wani abu ake ba su, yanzu in aka ce an tattare harajin nan sun koma wani asusun na daban guda ɗaya ana tunanin jami’o’i na Nijeriya ba za su iya ci gaba da gudanar da gine-gine da samar da abubuwa na zamani na bunƙasa ilimi da sauran abubuwa makamantan wannan na cigaba ba.”