Tue. Apr 1st, 2025

An Buƙaci Malaman Makarantun Sakandire Su Taimaka Wa Manufofin Gwamnatin jihar Kano

By Saleh Aliyu Dec 8, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Kwamared Abdullahi Usman Yalo shugaban ƙungiyar malaman makarantun Sakandire na jihar Kano, ya bayyana gamsuwarsa a kan abubuwa da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Alhaji Abba Kabir Yusuf take na fifita ci gaban ilimi a kan komai na rayuwa.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron walimar taya murna da ‘yan’uwa da abokan aiki suka shirya wa sabon babban Sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Kano, Kwamared Bashir Baffa da aka gudanar a harabar ɗakin karatu na Murtala Muhammad.

Ya ƙara da cewa, “Ko a kasafin kuɗi na shekarar da ta gabata saboda kulawar Gwamna kan ilimi ya ba da kaso 29.9. A bana kuma ya ba da kaso 31. Wannan abin a gode wa Allah ne ganin hankalin Gwamna da son sa na haɓɓaka ɓangaren ilimi.

“Sannan yana bai wa ma’aikatan ilimi fifiko. Ko wajen biyan albashi suna karɓa babu wata matsala. Don haka muna godiya gare shi da Kwamishinan Ilimi Haruna Doguwa da sauran masu ruwa da tsaki da suke taimaka mana domin samun nasara cigaban ilimi,” ya jaddada.

Abdullahi Usman Yalo ya ce wannan walima ta taya murna da ‘yan’uwa da abokai suka shirya wa babban Sakataren ma’aikatar ilimi Kwamared Bashir Baffa Muhamma, suna godiya ga Allah da ya kasance ɗaya daga cikin sune malamin makaranta, kuma kamar abin nan ne da Hausawa ke cewa ja ya faɗo, ja ya ɗauka aka yi, domin ita ma babbar Sakatare da ya gada ta baya da aka sauya mata ma’aikata, Hajiya Kubra Imam daga wajensu take, malamar makarantar Sakandire ce.

Shugaban ƙungiyar na Malaman Sakandiren na jihar, Abdullahi Usman Yalo, ya yi kira ga dukkan malaman makarantu su haɗa kansu gaba ɗaya ta yadda za su taimaka wa Kwamared Bashir Baffa domin su ga ya sami nasara wajen taimaka wa gwamnati domin samun nasarar ilimi a jihar Kano.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *