Tue. Apr 1st, 2025

Wajibi Ne Kawu Sumaila Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Da Dungurawa -Shugaban KYD

By Saleh Aliyu Nov 27, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban ƙungiyar cigaban matasa a siyasar Kano (Kano Youth Democrat), Malam Aliyu Sama’ila ya yi tir da matakin rashin biyaya da Sanatan Kano ta Kadu ya ɗauka kan shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashim Suleiman Dungurawa duk da cewa jagoranci jam’iyyar gaba yake da duk wani mai riƙe da kujerar siyasa a ƙasa.

Sama’ila ya ce sun yi mamaki mutuƙar gaske ganin yadda Sanata Kawu Sumaila yake aibata shugaban jam’iyyar NNPP a kafafen yaɗa labarai ganin cewa jam’iyya tana da damar ladabtar da duk wani ɗanta da ya kauce daga manofofin tafiyarta.

Ya ce, “A tsarin siyasar ƙasar nan duk wani ɗan jam’iyya da ya samu saɓani da wani a jam’iyya, uwar jam’iyyar ce take shiga tsakani. Saboda haka maganar da Hashim Dungurawa ya yi kan tsawatar wa Kawu Sumaila da ya daina shiga mahibban Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Kano abu ne da ke kan tsarin doka na tafiyar Kwankwasiyya”.

Shugaban na KYD ya ƙara da cewa, Sanata Kawu Sumaila ya tuna cewa al’umma ba su zaɓe shi ba sai da jam’iyyar NNPP ta hassale masa ya yi takara a cikinta, kuma sunan jam’iyyar har yau yake amfani a majalisar dokoki na ƙasa. “Hakan na nuwa cewa jam’iyya ce gaba da kowa a muƙamin da mutum ya tsinci kansa a kai zaɓaɓɓe,” in ji shi.

Aliyu Sumaila ya ƙara da bayyana cewa idan dai ba Sanata Kawu Sumaila yana da wata manufa ta daban ba kan shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano ya gaggauta janye ƙarar da ya shigar a kotu domin samun maslaha da cigaban jam’iyyar a Kano ta Kudu.

Ya ce suna sane da wani ƙullin da aka ɗauko domin wargaza haɗin kan jam’iyyar NNPP da take da shi a Kano domin biyan buƙatun wasu a Abuja. “Lokaci zai zo da za mu bayyana wa al’umma irin shirin da maƙiya cigaban jihar Kano suka ɗauko domin kassara tafiyar gwamnati Abba Gida Gida da jagoran jam’iyyar na ƙasa baki ɗaya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.” Cewar Sumaila.

“A ƙarshe ƙungiyar KYD da kuma tafiyar jam’iyyar NNPP a shiyyar Kano ta Kudu ba ma goyan Sanata Kawu Sumaila kan matakin da ya ɗauka kan shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, mu masu biyayya ne da tsarin uwar jam’iyya na ƙasa da jiha baki ɗaya,” cewar Aliyu Sumaila.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *