Tue. Apr 1st, 2025

Asibitin Ƙwararru Na Gombe Ya Ƙaryata Zargin Rashin Ruwa A Asibitin

By Saleh Aliyu Jun 9, 2024

Daga Abubakar Rabilu Gombe

Hukumar Asibitin Ƙwararru na jihar Gombe ta ƙaryata zargin da wani ya fito a gidan radiyo yana cewa babu ruwa a asibitin kuma ba wuta idan ka kai mai haihuwa sai ka sayi kurar ruwa wato kafin a karbi marar lafiyar.

Daraktan Asibitin Dakta Mu’azu Shu’aibu Ishaqa, a zantawarsa da Wakilinmu ne ya ƙaryata hakan inda ya ce ba gaskiya ba ne suna da wuta suna da ruwa a asibitin domin suna da borehole mai aiki da hasken rana da yake samarwa da asibitin ruwa a kowanne lokaci.

Ya ce duk da kwanakin baya an samu matsalar wuta da ta shafi ruwan sha a jiharsu a asibitinsu suna da ruwa wannan lamari bai shafe su ba.

Dakta Mu’azu ya ja kunnne ‘yan siyasa da cewa duk adawar su da gwamnati kar ya shafi asibiti, domin asibiti waje ne na al’umma da kowa zai iya zuwa jinya ba ruwan asibiti da siyasa ko a wacce jam’iyya ko addini kake za ka iya zuwa asibiti a maka jinya, amma yana mai kira ga wannan dan siyasa da ya janye kalamansa don hakan bata suna ne.

Ya ce a ‘yan kwanakin baya ne wani dan siyasa ya shiga gidan rediyo ya bayyana cewa ba ruwa a asibiitn ƙwararru, idan mutum ya kai marar lafiya musamman mai haihuwa sai ya sayi kurar ruwa wato kuskus mai jarka shida kafin a karbi marar lafiyar inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

A cewar sa gwamnati ta gyara asibitin an kuma samar da kayan aiki da ma’aikata ƙwararru an sanya fitilu masu aiki da haske rana wato solar a wasu sassan asibiitn dan saukake aiki a lokacin da ba wutar lantarki.

Daga nan sai ya ce tun kafa wannan asibiti a shekarar 1958 ba a taba samun ci gaba irin na wannan lokacin ba saboda hatta ƙwararrun likitoci da magunguna ma da ake da su sun fi na baya.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *