
Daga Hadi Bawa
Tsohon kakakin majalisar Kaduna ya musanta amincewa da bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Samar ciwo bashin Dala miliyan 350 daga Bankin Duniya
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, ya musanta ikirarin cewa majalisar ta tara karkashin jagorancinsa ta amince da amso lamunin Dala miliyan 350 na Bankin Duniya da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya karba.
A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti don binciki duk wani kudiri, lamuni da kwangilar da aka bayar, da kuma sauran ayyukan kashe kudade da kuma ayyukan da gwamnatin da ta shude ta fara aiwatarwa, tsakanin ,,shekarar 2015 zuwa 2023, a karkashin gwamnatin El-Rufai.
Kakakin majalisar, Yusuf Liman ne ya kaddamar da kwamitin mai wakilai 13 a zaman majalisar a ranar Talata.
Kafa kwamitin ya biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Kauru, Mugu Yusuf ya gabatar, inda ya bukaci majalisar ta binciki dukkan basussukan da gwamnatin El-Rufai ta amso.
Jaridar PUNCH ta ba da rahoton cewa Gwamna Uba Sani, a yayin wani taro da aka yi kwanan baya, ya koka da dimbin bashin da ya gada daga magabacinsa, El-Rufai, a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Sani ya ce an bar jihar da wasu ‘yan kudade da ba su taka kara suka karya ba, ba sa isar sa ya biyan albashi.
Ya kara da cewa gwamnatinsa ta gaji jimillar Dala miliyan 587 da rancen Naira biliyan 85 da kuma bashin kwangila 115 daga hannun tsohon gwamnan.
Sai dai yayin da yake kare zargin cewa majalisar da ke karkashin jagorancinsa ta amince da ciwo bashin Dala miliyan 350 na Bankin Duniya da El-Rufai ya amso, Zailani ya bayyana a wani faifan bidiyo da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga shugaban majalisar ya wallafa a ranar Laraba. Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Suraj Bamalli, tsohon kakakin majalisar ya dage cewa bai amince da lamunin ba.
Ya ce; “Na dade ina jiran wannan rana, kuma ga ta ta zo yau. Ba mu ba da izinin ciwo bashin nan ba. Wasu daga cikin abokan aikina suna kusa, kuma har yanzu shida daga cikinsu mambobi ne na wannan majalisa mai girma, ciki har da Isaac Auta Zankhai, tsohon mataimakin shugaban majalisar. A lokacin sai suka ce in amince da lamunin. Na ce a’a, muna bukatar mu san adadin bashin da ake bin mu ”
Idan za a iya tunawa, baya ga binciken duk wasu ayyuka na kudi, lamuni da kwangila da gwamnatin El-rufai ta bayar, majalisar dokokin jihar ta kuma umarci kwamitin da ya gayyato fitattun mutane da suka hada da tsofaffin shugabannin majalisun tarayya ta 8 da 9, da kwamishinonin kudi, da tsoffin manajan daraktocin kasuwannin Kaduna da kwamishinonin kasafin kudi da tsare-tsare da sauransu.