
- Ya Raba Buhunan Shinkafa Milyan Daya a Fadin Kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyarsa ta Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmin kimamin Dubu 10 kowace rana a jiharsa ta asali, wato Kano.
Har ila yau, gidauniyar ta kara wa’adin ne ta hanyar raba buhunan shinkafa Milyan Daya da kudinsu ya haura Naira Bilyan 13, a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, domin rage radadin yunwa a kasar.
Manufar hakan, kamar yadda gidauniyar ta bayyana ita ce, domin sassauta wa Milyoyin ‘yan Najeriya wahala a cikin kalubalen tattalin arziki a kasar.
Wannan baya ga rabon biredi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma 15,000 a kullum ga mazauna Legas, abincin da aka fara kuma ya dore tun 2020 a lokacin COVID.
Abincin da aka dafa na Ramadan kyauta ya hada da Shinkafa (dafa-duka), farar Shinkafa da miya, Dafa-dukan Taliya, Wake hade da kaza da kuma naman Shanu, a hada da kwalbar ruwansha ga kowane mutum.
Ana dai rarraba abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen gyaran hali da kuma gidajen marayu, da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.
Wani wanda ya ci gajiyar wannan tallafi da jinkan al’umma da gidaunyar ta Dangote ke yi, mai suna Musa Maikatako, mazaunin garin Tarauni, ya nuna jin dadinsa da wannan karamcin da ya ce ya taimaka ma sa wajen yin buda-baki cikin sauki.
Maikatako, wanda a bayyane yake cikin farin ciki, ya ce cin abinci kyauta zai rage wahalhalun da jama’a da dama ke fama da shi a yau, musamman ma idan aka yi la’akari da matsalar tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abincin zai taimaka matuka wajen tallafa wa talakawa, irin mu, ta yadda muke samun mu yi buda baki akalla tare da abinci mai kauri da za mu ci.
“Na san mutane da yawa a jihar nan wadanda za su iya yin buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan abincin ya kawo sauki,” in ji shi.
A lokacin da yake nuna farin cikinsa, Maikatako ya nuna godiya ga gidauniyar Dangote bisa wannan karimcin, inda ya yi addu’ar Allah ya kara masa arziki ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.
Wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata dauki.
Cewar Inna, ta yi farin ciki da an ba ta abinci mai daɗi kyauta a cikin wahalhalun da ake ciki.
“A cikin wannan wahalhalun da muke samu, ko da sau biyu a rana muke samun wahalar cin abinci, amma daga cikin shudin wata, wani ya gabatar mani da wannan abinci mai dadi, abin mamaki ne.
“Ba abin da zan ce sai dai in yi godiya ga ku da Aliko Dangote, ina rokon Allah Ya kara muku albarka.”
Baya ga rabon biredi da aka yi shekara 4 kyauta, an shafe sama da shekaru 30 ana ci gaba da ciyar da mabukata a Kano cikin nutsuwa da Aliko Dangote ya yi. An yi hakan ne daga gidan mahaifiyarsa da ke Koki da kuma wuraren dafa abinci daban-daban.
Wannan shirin ciyarwa yana ciyar da mazauna Kano 10,000 a kullum tare da karin kumallo, abincin rana, da kuma abincin dare, wani abin al’ajabi na musamman wanda aka kwashe sama da shekaru 30 ana yi.