Tue. Apr 1st, 2025

In Alfahari Da Karramawar Da Na Samu Saratu Gidado (Daso)

By Jaridar Amana Dec 13, 2023 #Nishadi
Daga Mukhtar Yakubu
A ranar asabar 9 ga Disamba 2023 aka yi bikin karramawa na Zuma Film Festival Award  wanda NFC wato Nigerian Film Corporation suka saba yi duk shekara a Abuja in da aka karrama jarumai da kuma fitattun ‘yan Nigeriya da suka bayar da gudummar su don ci gaban kasa a wani fanni na rayuwa da suka kware.
Fitacciyar jaruma a Kannywood Hajiya Saratu Gidado (Daso) ta na daya daga cikin fitattun ‘yan Nigeriya da aka karrama da kambun wadda ta bada gudummawar ta wajen ci gaban kasa wato ‘Lifetime Achievement Award’.
Wakilin mu a Kano  ya tattauna da ita a game da wannan karramawar da aka yi mata. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance.
Saratu Gidado (Daso) kamar yadda aka fi sanin ki, a ranar asabar din da ta gabata kin samu wani kambu na karramawa da hukumar ‘Nigerian Film Corporation’ a taron da ta gudanar, don haka muna son ki yi wa masu karatun mu karin bayani.
Daso  Wato Allah mai iko kamar yadda ka ce an karrama ni a zaben gwaraza da zan kira shi na duniya, don har da ma mutanen Ingila a ciki na gani sun zo daga Faransa da sauran kasashe duk sun zo mun yi hotuna ma da su. Kuma ni a arewa ni kadai ce aka zaba saboda sun ga cancanta ta a kan irin aiki na na sana’a ta ta fim  suka gayyace ni kamar yadda sakon ya zo mini ta Soshiyal midiya saboda duk yanzu na fi mayar da ayyukana a kan Soshiyal midiya don haka duk wanda yake so ya yi magana da ni ta Soshiyal midiya a ke samu na ba sai an tambayi wani lambata ba
To don haka wannan gayyatar ma ta Instagram suka yi mini magana, don haka sai na ji dadin karramawar saboda ban san su ba. kuma ban taba ganin su ido da ido ba, kawai a fim suka ganni suka ga cancanta ta ba tare da sun bi ta hannun kowa ba suka bi ta shafina na Instagram muka yi magana har suka turo mini kudin Jirgi suka samar mini da masauki kuma kafin wannan sun turo mini da katin gayyata na ranar da za a yi, kafin wata guda a yi taron, amma ban sanar ba saboda halin rayuwa sai ranar da za a yi na sanar. Kuma a yanzu Allah ya sa mun je an yi taro an tashi lafiya na dawo gidana tare da kambun karramawa da aka ba ni.
Da yake taron na Jama’a ne masu yawa da aka karrama ku, ko ya ya kika samu kanki a cikin wannan taron?
To gaskiya kamar yadda na fada maka ni kadai ce daga arewa a fannin sana’ar mu haka ma mutum daya ne daga kudu wanda shi bai samu zuwa ba, kuma duk wasu harkokin rayuwa daga arewa ma ni kadai ce na je wanda aka karrama sai dai wadanda aka gayyata don haka na ji dadin wannan karramawar sosai, saboda na wakilci arewa kuma na wakilci Kannywood, don haka wannan abin alfahari ne a gare ni.
Duk da cewar ba a wannan lokaci ba ne kika fara samun kambu na karramawa, ko me ya bambanta wannan da wadanda kika samu a baya?
E haka ne na sha samun karramawa, ina ganin tun da na shiga harkar fim ma na ke samun hakan, yau shekara 23 kenan ina samun kyautukan karramawa daga bangarori na jama’a da dama. Amma dai wannan shi ne mafi girma da na samu, saboda shi ne aka kira ni har zuwa Abuja don a karrama ni kuma aka hada mu da manyan mutane na duniya aka aka karrama mu, kuma shi ma kambun karramawar na musamman ne, don haka zan iya cewa wannan shi ne mafi girman karramawa da na samu a yanzu ban san nan gaba ba ko za a kira ni zuwa Ingila da Amurka don a karrama ni.
Kuma Alhamdulillahi wannan ya kara mini karfin gwiwar da na samu da zan ci gaba da harkar fim da aka sanni da ita. Domin irin wannan shi ne yake kara wa irin mu karfin gwiwa saboda ba don mun san wani ko wata hanya ba, kawai Allah ne ya sa aka ga mun cancanta aka ba mu, saboda an ga yadda nake a cikin harkar fim na mayar da abin sana’a ba wai na dauki abin da wasa ko wata kwalliya ba , kawai ina sana’a ne don na samu kudi na gudanar da rayuwata cikin mutunci. Don haka ina kira ga abokan sana’a ta ‘yan fim, su daure su ci gaba da kwazo kamar yadda muke yi, don su ma wata rana za a kira su a ba su wannan karramawar, domin kafin a ba ni na san an bai wa wadansu. Amma a wannan shekara ta 2023 Saratu Gidado (Daso) aka baiwa wannan babbar karramawa. Don haka su ci gaba da bada kwazo su dauki wannan sana’ar a matsayin sana’ar su kada a dauke ta don neman suna don ba a yin suna sai an zama gwarzo.
Sannan ina kira ga mutanen waje da suke kallon mu duk wadanda suke zagin mu su daina, idan kana kallon sana’ar mu a matsayin marar kyau, to kaima a wajen wani taka sana’ar ba mai kyau ba ce, don haka mu rinka yi wa junan mu adalci muna fatan Allah ya yi mana jagora.
To madalla mun gode.
Nima na gode.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *