Tue. Apr 1st, 2025

An dawo da wutar lantarki ga Radio Nijeriya Kaduna

By Gazali Haruna Jan 27, 2024 #Wuta

Hukumar Lantarki ta kasa ta dawo da wuta ga Radio Nijeriya Kaduna kwana guda bayan yanke wutar ba zato ba tsammani.

Shugaban Radio Nijeriya Kaduna Malam Buhari Auwalu, yace wannan dai ya biyo bayan naminijin kokarin Ministan yada labarai Alhaji Mohammed Idris Malagi da shugaban hukumar gidajen Radio Tarayya Dr. Muhammad Bulama

Malam Buhari Auwalu yayi bayanin cewa, ministan yada labarai ya bada muhimmiyar gudummuwa wajen aikin da hukumomin da suka dace ganin an karshen wannan matsala

Malam Buhari Auwaku yace Ganin irin gudummuwar da Radio Nijeriya Kaduna ke badawa wajen fadakarda al’umma ne yasa shugaban hukunar gidajen Radion Tarayya Dr. Bulama Mohammad da Minista suka yunkuro wajen tallafawa Radio Kaduna domin tabbatar da ba a Sami katsewar shirye shirye ba.

Daukar matakin gaggawa da kyakkwan tsari tare da aiki da hukumomin da suka dace sun taimaka gaya wajen maganin wannan matsala nan take.

Daga dai wannan yunkuri, Radio Kaduna da ya fi kowane Radio dadewa Yana bada gudummuwa a Arewa, zai ci gaba da aikin sa kamar yadda aka sanshi a cewa Malam Buhari Auwalu..

Yusuf Zubairu

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *