Tue. Apr 1st, 2025

Gwamnatin Zamfara Tana Na Jiran Shawara Ma’aikatar Shari’a Biyan Tsafin Mataimakan Shugabanin Kananan Hukumomi Da Kamsilolisu

By Gazali Haruna Jan 24, 2024 #Hakki #Zamfara

Daga Hussaini Yero

Kwamishinan Kananan hukumomi na jihar Zamfara, Injiniya Ahmed Garba Yandi ya ce suna jiran shawarar kwararru kan batun biyan alawus na sama da Naira biliyan 5 da kungiyar tsofaffin mataimakan shugabanin Kananan hukumomi da Kansiloli na Jamiyyar APC da ta sha kayi suka nemi gwamna Dauda Lawal na Jamiyyar PDP.da ya biyasu hakokin su.

Da yake amsa tanbayoyin manaima labarai a ofishin sa kan batun, Kwamishinan ya amince da karbar takardar bukatun nasu wanda daga bisani aka mika wa ma’aikatar shari’a ta jihar domin samun shawarwari akan koken nasu.

Injiniya Yandi, ya bayyana cewa, ma’aikatarsa ba za ta iya daukar wani mataki kan lamarin ba saboda la’akarin da doka ta shafa wanda dole ne a yi karin haske akanta.

Sai dai a nasa ra’ayin Injiniya Ahmed Garba Yandi ya yi mamakin da ya sa basu nemi a biya su alawus-alawus daga gwamnatin da baya da suka yi aiki da itaba,dan suna da isashen lokacin na biyan su kakokin su tunda sune sukayi ma aiki.a mukamin Siyasa .Amma da ace ma’aikata ne wannan muna da haki mu biyasu ,kuma yanzu haka munbiyasu hakokin su ,su ma’aikatan da gwamnatin baya ta gaza biyan su nasu hakokin,na Albashi, alawus da na wadanda suka aje aiki.

Kwamishinan ya jaddada cewa, ma’aikatar za ta yi hakuri ta dauki matakin da ma’aikatar shari’a za ta bayar kan batun kafin daukar mataki na gaba.

Idan dai za a iya tunawa kungiyar tsofaffin Shugabannin Kananan hukumomi da kansilolin jihar Zamfara,karkashin mulkin tsohon gwamna Mtawale sun bukaci tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta biya wa mambobinta sama da Naira biliyan 5 na alawus-alawus din sallamar wadanda ta ce suna matukar bukatar tallafin kudi domin kula da iyalansu.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *