Daga Ibrahim Muhammad Kano
An yaba da matakin da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ɗauka ta ƙarƙashin Ma’aikatar slSufuri na haɗe kan ƙungiyoyin masu baburan A Daidaita Sahu guda 24 waje ɗaya suka zama guda ɗaya masu magana da murya guda da ake kira VOTORA.
Sabon Shugaban riƙo na ƙungiyar muryar masu baburan A Daidaita Sahu da mamallakansu na jihar Kano Voice of Trycles Owners and Riders Association Kano State, Kwamared Nazif BK Gidan Kuɗi ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya ce yanzu ƙungiyar da yake wa jagoranci VOTORA da ƙunshin mataimakansa guda 19 da dattawan ƙungiya 11 suna magana ne da murya ɗaya, sun kuma sha alwashin haɗa kai da su da sauran shugabanni na jiha da ƙananan hukumomi da na unit -unit na baburan A Daidaita Sahu da yardar Allah za su taimaka wa gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro wurin daƙile duk wani ƙalubale da matsaloli da ake samu a cikin harkar A Daidaita Sahu nan ba da jimawa ba.
Kwamred Nazifi BK Gidan Kuɗi ya ce, a matsayinsu na shugabannin riƙo na ƙungiyar VOTORA, babban saƙonsu ga mambobin ƙungiyar shi ne na godiya bisa irin haɗin kai da suke samu daga gare su a kowane lokaci.
Ya yi fatan su cigaba da ba su goyon bayan da ya kamata a duk lokacin da suka kira su a kan wani abu da ya shafi sana’arsu na kawo gyara. “Muna roƙon matuƙa da mamallaka baburan A Daidaita Sahu su amsa kira su yi biyayya ga abin da zai kawo musu cigaba da kare mutunci da kimar sana’arsu a jihar Kano.