Tue. Apr 1st, 2025

Ɓata-Gari Sun Auka Wa Mutane Bayan Rabon Kayan Tallafi Da Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi A Kano

By Saleh Aliyu Feb 21, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Wasu gungun ɓata-garin matasa sun yi yunƙurin ƙwace kayayyaki da wayoyin al’umma bayan rabon tallafi da ɗan majalisar tarayya na Fagge Muhammad Bello Shehu ya yi a gidan gwamnati.

Shaidun gani da ido a lokacin da abin ke faruwa sun ce gungun wasu matasa ne a bakin gidan gwamnatin suka far wa mutane suna yunƙurin ƙwacen waya da kayan da aka bai wa wasu da suka amfana daga tallafin.

Wata majiya ta ce yawancin ɓata-garin matasan ba ‘yan ƙaramar hukumar Fagge ba ne, wasu gungun haɗakar ɓata-gari ne daga wasu ƙananan hukumomin ƙwaryar birni da suka haɗu a yayin taron raba tallafin suka shiga ƙwacen.

Ɗaukin gaggawa da jami’an tsaro suka kawo suka tarwatsa gungun matasan ya bayar da kariya ga al’umma.

Mutane da dama sun yi kira a. kan lallai a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki na zaƙulo ɓata-garin matasan da hukunta su domin hana faruwar hakan a gaba.

Wani da muka tattauna da shi kan lamarin ya ce, ya zama dole gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kai, duba da cewa a kusa da gidan gwamnati da ake da tsaro an far wa mutane da ƙwace a taron raba tallafi, idan za a yi a wani waje daban za a iya fuskantar barazana makamancin wannan muddin ba a ɗauki mataki ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *