Daga Ibrahim Muhammad
Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta ce ya fahimci ƙoƙarin da Kwankwaso yake na shigowa cikinta ne ya sa Abdulmumin Jibrin Kofa ya fara kiraye-kirayen a sami sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
“Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Kofa ya zo da ita, yaudara ce. A siyasance ba ma buƙatar yin siyasa tare da Kwankwaso”.
Kakakin jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Ahmad S. Aruwa ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya ya yi da wani gidan radio da ke Kano.
Ya ce, “So suke su dawo APC don su ƙwace ta daga wajenmu. Domin Kwankwaso ya saba yin hakan tun da ya yi wa Malam Ibrahim Shekarau da dole sai da muka bar masa APC muka koma PDP. Haka kuma ya sake yi musu a PDP. Don haka mun gano wayon.
“Idan da gaske ne, Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya kamata ya daidaita Kwankwaso da Ganduje, amma ba Kofa ba.
“Idan ka lura da yadda Kofa ya zayyano muƙaman da Kwankwaso ya riƙe da waɗanda Ganduje ya riƙe za ka gane shi (Kofa) ya yi kaɗan ya ce zai sulhunta Kwankwaso da Ganduje,” in ji Aruwa.
Don haka ya ce su ba sa buƙatar yin sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje saboda daga ƙarshe cewa za a yi a haɗe, kuma in an haɗe su za a cutar.
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa a ƙarshen makon da muke bankwana da shi ya ce ya zama wajibi a sulhunta Ganduje da Kwankwaso saboda cigaban jihar Kano.