Tue. Apr 1st, 2025

Jami’ar KHAIRUN Wani Ɓangare Ne Na Ayyukan Marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u -Farfesa Abdulrashid Garba

By Saleh Aliyu Dec 31, 2024

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

“Jami’ar Khalifa Isyaka Rabi’u an samar da ita ne bisa tunanin Khalifan Tijjaniyya marigayi Sheikh Isyaka Rabi’u ne, wanda shi ne ya ƙirƙiro ta ta zama kuma cikamakin ayyukan alkhairi da yake yi kamar yadda aka san shi a yaɗa karatun Ƙur’ani da haddar sa da gina masallatai da masallatan da kyautata wa limamai da sauran abubuwa, haka ma ya yi wa karatun zamani hidima ta kafa makarantar Firamare da ƙaramar Sakandire da babba sai kuma ya ƙirƙiri Jami’a.”

Shugaban Jami’ar KHAIRUN, Farfesa Abdulrashid Garba ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a Kano.

Ya ce Allah cikin ikon sa bai nufa Khalifa zai ga Jami’ar ta soma gudanarwa yana raye ba, amma sai Allah ya wadata shi da ‘ya’ya nagartattu suka zo suka ɗauki lamarin tafiyar da ita, suka samar mata lasisi daga gwamnatin tarayya, aka kafa duk abubuwa na shugabanci, kama daga kwamitin amintattu ƙarƙashin Emiratos Farfesa Sani Zahraddeen da na zartarwa ƙarƙashin Farfesa Isyaku da na gudanarwa a ƙarkashin shugabancinsa.

Ya ce da suka zo Jami’ar a cikin watan 4 na watan Agusta shekarar 2024 suka yi ta ƙoƙarin su ga karatu ya kankama, suka ci gaba da zaƙulo mutane da za su zo su riƙe musu tsangayoyinsu na ilimi, suka ɗauki ɗalibai, bayan sun je Abuja sun gama ganin duk wanda ya kamata a kan a ba su amincewa za su ɗebi ɗalibai, suka zo suka ɗebi ɗalibai suka fara karatu a watan 2 na 2024. Sannan suka ƙirƙiro majalisar Dattawa ta Jami’ar wacce ita ce ruhinta.

Farfesa Abdulrashid Garba ya ce, sun samar da duk abin da ake buƙata na Jami’a, suka fara karatu. Allah yana ba su nasarori yanzu har sun gama shekarar ilimi ta farko, yanzu sun shiga ta biyu sun ɗebi ɗaliban farko guda 100, yanzu sun ɗebi na biyu su wajen 700 suna nan sun fara karatu.

Ya ce a cikin irin hikima ta Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u sai ya yi niyyar ya kafa Jami’a don ya samar da masana a guraben da babu su a Kano da yawa, sai ya ga abin da ya fi dacewa a karkata aƙala a kan abin da ya shafi Kimiyya da Fasaha.

Ya amince a fara da harkokin kula da lafiya a ɓangarori daban-daban aka yi Tsangaya ta ɗaya mai darussa uku, ta biyu ta fasaha da mai darussa uku. Sai Tsangayar Kimiyya da kwamfuta da yake da darussa 10. “A yanzu dai Jami’ar na da Tsangayoyi uku darussa 16, kowanne kuma na da shugaban sashe, wanda Farfesa ne, ko wanda ya kusa zama Farfesa. Dama duk shugabannin tsangayoyi Farfesoshi ne,” inji dji.

Ya ƙara da cewa sun ma fara yunƙuri na kafa Tsangayar shari’ar Musulunci, har sun ɗauuki shehin malamin da zai assasa musu. “Da zarar an fara shekarar karatun 2025 za su buɗe, tare da fara neman ɗaukar masu karatun Lauya. Jami’ar za ta zama tana da tsangayu guda huɗu da darussa 17,” ya tabbatar.

Ya ƙara da cewa dukkan tsangayoyin na Kimiyya da Fasaha ne zunzurutu, sai kuma na sharia da suke ƙoƙarin sa wa shi ma saboda shari’ar Musulunci suke so su yi domin wasu sai su je waje su yi karatun shari’ar Musulunci, amma sai su zo ƙasar nan a hana su shiga kotu, wannan ba abu ne mai daɗi ba, shi ya sa suke so su yi ta yadda za a bar su su shiga kotu ko a matsayin alƙalai ko lauyoyi.

Ya ce Jami’ar ta KHAIRUN ta yi duba da tarbiyya ta gidan Khalifa na Ƙur’ani da kasuwanci, sai suka shigo da tsari a Jami’ar ko me ka zo karantawa cikin darussa 16, lallai duk mako sai ka yi karatun Alƙur’ani, kuma suna bibiya idan ba ka yi ba, idan aka zo wani zangon karatu sai ka nanata, kuma za a ba kowanne shaida na darasi da ya yi na Ƙur’ani, sun kuma gina wajen koyar da sana’o’i da za a riƙa koyawa ɗalibai sana’o’i, zai zamana duk wanda ya gama Jami’ar zai fito ya iya dogara da kansa.

Ya ce wani bambancin su da sauran jami’oi shi ne, duk ilimi idan babu tarbiyya shirme ne, shi ya sa duk yaron da ya shigo Jami’ar sai an ƙarfafa shi a kan tarbiyya, “In ka sami ilimi ka iya mu amala da Ubangiji ta jin tsoronsa da girmama iyaye da abokai da kyautatawa tsakanin mace da mijinta da duk kyawawan ɗabi’u abin da suke koya musu ke nan, a ɓangaren tarbiyya shi ya sa digiri da suke bayarwa ya bambanta da sauran.

Shugaban Jami’ar KHAIRUN Farfesa Abdulrashid Garba ya ce, a lokacin da gwamnatin tarayya ta ba da izinin a gina Jami’ar sai kuma ta sahale a zo a gina cibiyar ƙasa da ƙasa ta nazarin Kimiyyar Alƙur’ani da yanzu take ƙarƙashin kulawar Barista Ɗan’almajiri ta fara da tattaro Alarammomi 88 an yi ganawa da su saboda suna so su haɗu da su su mori darajar Ƙur’ani da Allah ya ba su, su kuma su mori zamananci da za su bijiro musu da shi.

Ban da wannan sun kira wata yarinya da ta yi na ɗaya a musabaƙar Ƙur’ani ta duniya ta zo Jami’ar sun girmamata.

Cibiyar tana da muhimman shirye-shirye guda huɗu da za ta gudanar. Na farko tana so ta yi musabaƙar Ƙur’ani na bebaye. Na biyu na kurame. Na uku tana so ta yi taron Alarammomi mata. Sannan tana so ta yi musabaƙar rubutun Alƙur’ni bambancinsu da wanda ake karantawa idan an zo ba karatun za a yi ba, in an karanto maka rubutawa za ka yi kamar yadda ake satu. Alarammomi gwanaye ne za su zo su duba su yi alƙalanci.

Daga cikin tsare-tsaren da suke da shi, wajibi ne ma’aikatan Jami’ar sai sun yi karatun Ƙur’ani ana koyar da karatun na kwana ɗaya a mako. Akwai Malama da take koya wa mata da malami na ajin maza da ake koyawa ma’aikatan Ƙur’ani.

Farfesa Abdulrashid Garba ya ce, Jami’ar ana gudanar da ita ne ba don riba ba. Shi ya sa ma kuɗin makarantar ya zama mafi sauƙi a dukkan jami’o’i da suke kwasa-kwasai irin nasu a ƙasar nan.

Abdulsalam Isyaka Rabi’u ya biya rabin kuɗi ga ɗaliban farko, sannan ya ɗauki nauyin mutum 500 za su yi karatu kyauta. Sannan babu abin da ake buƙata akwai ɗakin gwaje-gwaje da na karatu da na harkar yanar sadarwa.

Ɗakin kwanan ɗalibai guda bakwai ne na maza da na mata, kuma tsarin ɗakunan nasu na yadda ake a makarantun Sakandire ne, ba su yarda da ware ɗaki ga ɗalibai ba.

Ya ce, “Akwai lokacin shiga da na fita da na kashe wutar lantarki da lokacin shiga da na fita daga makwanci. Kafin iyaye su kawo ‘ya’yansu suna sanar da sharuɗɗan Jami’ar in sun yarda su kawo ‘ya’yansu. Shi ya sa ba sa saka kuɗi da yawa.”

Furofesa Abdulrashid Garba ya yi fatan Allah ya sa jagorancin da suke a Jami’ar ta KHAIRUN yadda aka ba su amana sun karɓa, kuma da yardar Allah za su riƙe amanar bisa gaskiya da adalci.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *