Tue. Apr 1st, 2025

Sheikh Jingir Ya Buƙaci Matasa Su Dage Da Neman ilimi

By Saleh Aliyu Dec 30, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga al’umma musamman matasa su dage a kan neman ilimi na addini da na sana’a domin zai sa su tsira daga ganganci da wauta.

Shehin Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabinsa buɗe musabaƙar Alƙur’ani da ƙungiyar ta shirya na jihohi sama da 20 na Nijeriya da wasu daga maƙwabtan ƙasashe da za a shafe tsawon kwanaki bakwai ana yi a Jami’ar Bayero da ke Kano da ake sa ran ‘yan takara 130 ne za su yi musabaƙar a mabanbantan Hizufi.

Sheikh Jingir ya yi nuni da cewa idan mutane ba su yi karatun ba za su zama ruwan tushe idan aka yi duba da jihar Kano mai ƙananan hukumomi 44, amma jihar Bayalsa da ita dattawansu a majalisa uku-uku ne wato Sanata uku a Bayalsa, haka ma uku a Kano don ana barci.

Ya ce sun zaɓi Kano ne domin gudanar da musabaƙar a karo na bIyu saboda fice da ta yi a sha’anin addini irin abin da Allah ya yi wa Kano na albarka da alkhairi shekaru masu yawa da suka gabata idan aka taro mahaddata Alƙur’ani tun daga Arewa mai faɗi Kanawa sun fi kowa yawan mahaddata.

Ya ce Musulunci ya kafu a Kano, don haka ƙungiyar Izala sananniyar ƙungiya ta addinin Musulunci da yake jagoranta, wacce tun daga gabatar da ƙungiyar da Marigayi Sheikh Isma’ila ya yi da shawarar babban malamin su Marigayi Sheikh Mahmud Gumi a Jos shekaru 47 ke nan ake ta yaɗa addini.

Sheikh Jingir ya ce tun daga gabatar da ƙungiyar babu ranar da wa’azi ya yi baya sai daɗa gaba gaba da taimakon Allah. “Ƙungiya ce ta wa’azin Musulunci da take dogara da hujjojin Ƙu’ani da Sunnah,” in ji shi.

Ya ce karatun Ƙur’ani alkhairai da ke ciki Allah ne kaɗai ya san su, bayan muhimmancin karatun Ƙur’ani da fahimtarsa dole sai an yi aiki da shi ba wai ka san yadda za ka karanta daidai ba akwai. Babban aiki shi ne yin aiki da abin da yake karantar da mu na shiriya,” ya jaddada.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yaba wa gwamnatocin Kano na baya da na yanzu, musamman kan hidima da take wa Ilimi ta tura ɗalibai su nemi ilimi ƙasashe daban -daban da dukkansu ‘ya’yan talakawa ne.

Ya jaddada kira ga matasa maza da mata su karanta Ƙur’ani su yi aiki da shi.

Musabaƙar ta bana dai za a gudanar da ita ne a sassa shida Hizifi huɗu da Tajawid da Hizifi 10 Tangimi da 20 da 40 da Tajawid da Hizifi 60 da ruwayoyi guda huɗu da Tafsir da iya rubutu tambayoyi, kamar yadda shugaban kwamitin musabaƙar Malam Hafiz Aminu Yusuf Nuhu ya bayyana.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *