Wani ɗan jarida daga Katsina, Abubakar Ayuba Masanawa, wanda ke jagorantar kafar yaɗa labarai ta Ɗanmasani Radio Online, ya yi kira ga Hukumar Katsina State Contributory Healthcare Management Agency (KATHCIMA) da ta yi koyi da ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi wajen kawo sauye-sauye a ɓangaren kiwon lafiya, musamman a cikin wannan lokaci na ci gaban da ake samu a jihar.
Masanawa ya bayyana cewa, sauye-sauyen da ake samu a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, suna da muhimmanci wajen inganta rayuwar al’umma da samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Ya yaba da yadda gwamnatin ke ɗaukar matakai na inganta fannin lafiya, wanda hakan zai kawo ci gaba mai ɗorewa a jihar Katsina.
Ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda wasu ma’aikatan lafiya ke sakaci da aikinsu, wanda hakan ya janyo asarar rayukan ‘yan-biyun da uwargidansa ta haifa masa.
A cewar Masanawa, wannan abu na faruwa ne sakamakon rashin ɗaukar matakan da suka dace a lokacin da ake buƙata, wanda hakan yana nuna rashin ingancin tsarin kiwon lafiya a wasu sassan jihar.
Ɗan jaridar ya yi kira ga Hukumar KATHCIMA da ta gudanar da bincike kan wannan lamari, ta ɗauki matakan da za su hana faruwar irin wannan sakaci a nan gaba.
Ya jaddada cewa akwai buƙatar gyara cikin tsarin kiwon lafiya da kuma samar da isassun kayan aiki da ma’aikatan lafiya masu kwarewa, domin samun ingantacciyar kulawa ga al’ummar jihar.
A ƙarshe, Masanawa ya yaba da ƙoƙarin Gwamnan jihar Katsina, wanda ya kai ziyara asibitin, wajen sauke nauyin da ke kansa, tare da tabbatar da ci gaban jihar a ɓangarori daban-daban, musamman a fannin kiwon lafiya.
Ya yi addu’a ga Allah ya taimaki Gwamnan da al’umma baki ɗaya, domin samun ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya a jihar.