Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan Boye, ya ƙaddamar da duba masu larurar idanu kyauta ga al’ummar yankin a Asibitin Gwagarwa a safiyar ranar Asabar.
Da yake bayani game da shirin shugaban lafiya jari na ƙaramar hukumar, Hon.Muktar da aka fi kira da Wazobiya ya yaba wa shugaba ƙaramar hukumar Nasarawa, Ogan Boye, bisa wannan tsari da ya ɗauko na kwaikwayon jagoransu na siyasa, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso na manufarsa ta jajircewa a kan ilimi da lafiya.
Ya ce, “Ogan Boye ya ɗauko irin wannan aƙida ta ba da kulawa a kan lafiya da ilimi domin zuwan sa ya yi abubuwa da dama kan lafiya. Duk wani abu da za a yi na lafiya yakan kirawo su a matsayin nasu kula da lafiya jari a yi shawarwari da su, kuma cikin ikon Allah ana samun nasara.”
Wazobiya ya ce wannan taimako na duba lafiyar idanu da ake yanzu irin mutane da suka taru sai ka ga wanda kake ganin kamar kalau yake, amma sai a same ba shi da lafiya. Ya yi fata Allah ya saka masa da alkhairi.
Ya yi nuni da cewa yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika gwarzo komai ake buƙata yana yi, su ma a ƙaramar hukumar Nasarawa, Ogan Boye yana koyi da shi, komai ake buƙata shi ma yana yi. “Muna alfahari da shi. Muna sa ran duk wanda ya zo aka duba idanunsa za a yi masa aiki da ba su magani kyauta, wanda ƙwararrun likitoci ne na ido da suka zo daga ƙasashen duniya suke wannan aiki na duba idanu da za a shafe kwanaki ana yi,” ya jaddada.
Shi ma Kansilan lafiya na ƙaramar hukumar Nasarawa, Malam Abdul Hamid Musa ya gode wa Allah da kawo aikin idanun ƙaramar hukumar da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Yusuf Imam Khan Boye ya yi dama hakan na daga cikin irin kuɗure-kuɗuresa na taimaka wa al’ummar yankin, wanda hakan koyi ne da yake da manufofin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da tsarin Kwankwasiyya.
Ya ce harkar lafiya a ƙaramar hukumar Nasarawa na samun kulawa ta musamman tun zuwan Ambasada Ogan Boye, wanda kullum tunaninsa shi ne ɓullo da yadda za a taimaki na ƙasa, kuma ana nan ana ta tsare-tsare da za a taimaki al’umma.
Malam Abdulhamid Musa ya ce, yanzu haka ma idan aka zagaya asibitocin ƙaramar hukumar ana nan ana aikace-aikace, “Dama shugaban ƙaramar hukumar ya ba da umurni a kawo masa bayani na duk asibitocin da ke yankin da abubuwa da ake da buƙata na gyara a cikinsu a kawo musu kayan aiki na zamani nan da ɗan lokaci kaɗan za a ga sauyi a asibitoci a ƙaramar hukumar,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa da su da suke taimaka masa suna zagayawa domin ganin yadda ma’aikatan lafiya ke kula da ayyukan su akai-akai yana kuma yabawa da ƙwazon su har ma yakan yi musu kyauttuka. “Mu ma muna shiga muna gani. Mun yaba da yadda jami’an lafiya ke aikinsu ba dare ba rana don inganta lafiyar al’ummar Nasarawa,” ya ce.
Kansilolin Dakata da na Gawuna da wasu daga cikin jami’an ƙaramar hukuma sun kai ziyarar gani da ido wajen aikin duba masu larurar idanun sun yaba da yadda aikin ke gudana.