Mon. Mar 31st, 2025

Sabon Ajiyan Kano Ya Yi Alƙawarin Ci Gaba Da Hidimta Wa Al’umma

By Saleh Aliyu Oct 29, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Ajiyar Kano Sarkin Fulanin Shanono, Alhaji Ja’afar Muhammad Shanono ya ce za su ci gaba da ba da gudunmawa kamar yadda ya saba a mahaifarsa ta ƙaramar hukumar Shanono wajen hidimta wa jama’a ta fanninn ci gaban Ilimi, kiwon lafiya, ruwan sha da sauran abubuwa tun kafin wannan naɗin.

Ya bayyana hakan ne da yake zantawa da ‘yan jarida bayan naɗin da Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi ll ya yi masa a fadarsa a matsayin sabon Ajiyar Kano.

Ya ce shi ba shi da ta cewa sai godiya ga Sarkin Kano Khalifan Tijjaniya Muhammad Sanusi saboda dawo musu da wannan sarautar tasu da ta daɗe ba ta gidansu, amma ya zama sababin dawowarta gidan.

Alhaji Ja’afar Muhammad Shanono ya ce halayyarsa masu nagarta da Sarki ya bayyana ya san su ne saboda yi aiki da Maimartaba Sarki Muhammad Sanusi tun yana Gwamnan babban bankin ƙasa a matsayin mataimakinsa na musamman tsawon shekaru biyar har a halin yanzu kuma shi yana ci gaba da yi wa ƙasa hidima a bankin na ƙasa.

Ajiyar Kano Sarkin Fulanin Shanono, Alhaji Ja’afar Muhammad Shanono ya bayyana godiya ga jama’a bisa irin dafifi da suka yi na taya shi murna wanda soyayya ce ta kawo hakan wanda Allah ya yi wa arziƙin mutane sai ya gode wa Allah.

Ajiyar na Kamo ya jaddada godiya ga Allah da masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarki Malam Muhammad Sanusi ta yi da hakimai da duk sauran jama’a da suka zo don taya shi murna.

Ita ma ɗaya daga cikin ƙanne shakikai ga sabon Ajiyar Kano da aka naɗa, Hajiya Hadiza Magaji Buhari ta ce, suna farin ciki mutuƙa da godiya ga Sarkin Muhammad Sanusi da wannan karamci da dama da ya yi masu.

Ta ƙara da cewa su sun san Ajiyan Kano mutum ne da yake abubuwa da dama na taimaka al’umma, duk wanda yake shiga Shanono zai ga ɗimbin ayyukansa, kama daga samar da ruwan sha, makarantu, taimaka wa mata da marayu da sauran fannoni ba kawai a Shanono kaɗai ba da sauran wurare.

Hajiya Hadiza Magaji Buhari ta ce tana da tabbacin ɗan’uwan nata zai ci gaba da hidima da yake ga al’umma, kuma tana bai wa al’ummar Shanono tabbacin sun sami ɗa mai mutunci da kishi na ci gabansu.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *