Daga Ibrahim Muhammad
Ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. MB. Aliyu ya tallafa wa kiristoci iyayen marayu da kayan abinci domin su sami yin bukin Kirsimeti da na sabuwar shekara cikin walwala.
Tallafin shi ne irin sa na farko da da aka soma yi a ƙaramar hukuma da ya sanya jin daɗi da farin ciki ga waɗanda suka amfana.
Ɗan majalisar ya bayyana dalilin tallafin shi ne ganin an zo ƙarshen shekara, wasu za su yi tafiya ta ziyara garuruwansu su yi bukin Kirsimeti, wasu kuma a nan za su yi, hakan ya sa ya ga ya kamata ya ba da wannan tallafi na kayan abinci.
Hon. MB. Aliyu ya yi nuni da cewa lokacin Azumi da Sallah suna yin irin wannan rabon tallafi, amma ba su taɓa tunawa da su ba kiristoci da suke tare da su ba sai wannan karon ta ƙarƙashin mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Joshua Mai Fata, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar Northern Minority Tribe, ya ga ya kamata su taimaka wa iyayen marayu da ‘ya’yan marayu na kiristoci.
Ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa a majalisar dokokin jihar Kano ya ce don haka ya ga dacewar ya ba su wannan tallafi na kayan abinci da kuɗin cefane N150,000 da wanda za su yi riguna N50,000.
Ɗaya daga cikin iyayen marayu da suka amfana da tallafin Madam Rabecca Betrus cikin jin daɗi da shauƙi ta ce tunda take a jihar Kano ba su taɓa samun irin wannan taimako da wani ɗan majalisa ba a matsayinsu na kiristoci sai wannan karo da ɗan majalisarsu na karamar hukumar Nasarawa, Hon. MB. Shehu ya ba su.
Ta yi addu’a da fatan alheri ga ɗan majalisar a kan kulawa da farin ciki ya sasu na ba su tallafi.