Tue. Apr 1st, 2025

Ɗan Majalisar Tarayya Na Fagge Ya Yi Rabon Tallafi Ga Al’ummarsa Sama Da 3000

By Saleh Aliyu Feb 20, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da raba tallafin kayan dogaro da kai da jari da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge, Hon. Barista Muhammad Bello Shehu ya samar ga al’ummar mazaɓarsa.

A yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar Kano, Gwamna Abba Kabir ya yaba wa ƙoƙarin ɗan majalisar tarayyar na Fagge MB. Shehu a kan bunƙasa rayuwar ɗimbin matasa ta samar musu ta hanyoyin dogaro da kai da ayyukan yi da bunƙasa harkar ilimi.

Gwamna Abba Kabir ya yaba da irin goyon baya da al’ummar Fagge ke bai wa gwamnatin Kano, sannan ya yi alƙawarin samar musu da ƙarin damarmaki na bunƙasa rayuwarsu.

A jawabinsa tun da fari ɗan majalisar tarayya na Fagge Muhammad Bello Shehu ya ce rabon na daga matakin cika alƙawari da ya yi lokacin yaƙin zaɓe na samawa ɗimbin matasa aiki da gudanar da ayyuka na bunƙasa cigaban yankin ƙari a kan kare muradunsu da na jihar Kano a majalisar tarayya.

MB. Shehu ya yi kira ga waɗanda suka sami tallafin su yi amfani da shi ta yadda zai amfane su da ‘yan’uwansu da sauran jama’a.

Daga cikin tallafi da ɗan majalisar tayayyar na Fagge ya bayar da mutane sama da 3000 a ɓangarori daban-daban sun haɗa da jari ga matasa, motoci, babura ga matasa da masu buƙata ta musamman da sauran abubuwa da dama.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *