Wed. Apr 2nd, 2025

Ɗan Majalisar Ƙasa Ya Raba Tallafin Kayan Noma A Kano

By Saleh Aliyu Dec 26, 2024

Daga Ibrahim Muhammad.

A ƙoƙarinsa na bunƙasa harkar noma a tsakanin al’ummar mazaɓarsa Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Hassan Husaini Tudun Wada ya ƙaddamar da rabon irin noma.

Daga irin noman da Ɗan Majalisar na Tarayya na Nasarawa ya raba akwai na masara, gero, shinkafa da kuma takin zanani da sauran kayayyaki na aikin noma.

Bayan tallafin noman da Ɗan Majalisar Hassan Hussain ya raba, kuma ya raba wa ƙarin ɗalibai guda 15 takardar shaidar shiga Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, wanda ƙari ne a kan ɗaliban da ya ɗauka a baya.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *