Mon. Mar 31st, 2025

Mangal Jagora Ne A Fannin Kasuwanci Da Siyasa -Ɗanmarna

By Saleh Aliyu Nov 17, 2024

An bayyana fitaccen ɗan kasuwan nan na ƙasar nan, Alhaji Barau Ɗahiru Mangal da cewa Uba ne ta fannoni daban-daban kama daga siyasa, kuma babban jagora ne a harkar kasuwanci.

Alhaji Sarki Usman Ɗahiru Shugaban Kamfanin DANMARNA Petroleum ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a fadar Sarkin Kano a lokacin ɗaurin aure da aka yi na ɗan Alhaji Ɗahiru Mangal da ɗiyar tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ya ce ɗaurin auren rana ce mai tarihi a wannan gari na Kano da aka tara ɗimbin jama’a domin shaidar wannan ɗaurin aure na iyalan Kwankwaso da na Ɗahiru Mangal an zo daga sassa daban-daban na ciki da wajen ƙasar nan.

Shugaban kamfanin man fetur na DANMARNA ya ce a matsayin Kano da take babbar uwa a ƙasar Hausa, wannnan taro ya ƙara fito da martabarta da karamcinta wajen karɓar baki. Kuma ya yaba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa ayyuka da yake na cigaban jihar Kano.

Alhaji Sarki Usman Ɗahiru ya ce wannan aure da ya haɗa iyalan ɗan siyasa da na ɗan kasuwa da ma tafiya ce da suke kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjumai ne, kasuwanci na tafiya da siyasa, kuma yanzu tafiya ce ta cuɗa ni in cuɗe ka, don haka wannan abin alfahari ne da farin ciki bisa gagarumin wannnan haɗi da aka yi, komai ya yi daidai muna yi musu fatan alkahiri da fatan samun zuriya ta gari.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *