Daga Ibrahim Muhammad
Ambasada Abba Hassan Baban Maja Sarkin Tsuntsayen Hausawan Afirka, kuma Shugaban ƙungiyar shigar manoma ta Gida-Gida All Farmers Associations, sun gudanar da taron koyawa matasa da iyaye mata yadda za su riƙa noma da kiwo a gidajensu.
Ya ce sukan zo lokaci-lokaci suna horar da mutane a kan abin da ya shafi kiwon kaji da yadda za su kula da su a yanayin zafi ko sanyi, sannan sun koya wa mata da matasa samar da 1000 yadda za su shuka dankalin Turawa a yayin taron da aka yi na yini ɗaya a Kano.
Ya ƙara da cewa suna yin irin wannan taron tun sama da shekara 20 domin farfaɗo da sana’ar noma da kiwo da suka gada kaka da kakanni ta ba su dukkan wani arziƙi a baya, shi ya sa yanzu saboda ilimin noma na sauyin zamani suke gayyato mata da maza domin a ba su horo kan fasahar noma na zamani.
Ya ce wannan horo na tasiri wajen haɓɓaka tattalin arziƙi domin za a rika noma a unguwanni da kangwaye mace a tsakar gidanta zata iya noma duba da yanda gonakin ma sukayi tsada kuma zai samar da tsaro idan aka yi la’akari da matsalar tsaro da take hana zuwa gonakin su kuma ya samawa matasa aikin yi.
Ya ce tun suna yin wannan horo da mutanen da ba su fi 10 ba, har ta kai wuraren da suke kamawa ba ya isa saboda yawan jama’a, kuma kusan duk abin da suke kyauta ne, illa iyaka mutane na ɗan ba da kuɗaɗe da ake haɗawa a kama wuri da za a yi horon. Kusan komai shi yake ɗaukar nauyinsa da kuɗinsa, kuma an yi irin wannan horo daban-daban sama da sau 12.
Ambasada Baban Maja ya ce, tunda yake ba da wannan horo gwamnati tun daga kan ta ƙaramar hukuma ta jiha da ta tarayya babu wani Kansilan ko shugaban ƙaramar hukuma, ɗan majalisar jiha na tarayya ko wani Sanata ko Gwamna ko muƙarrabansu da ya taɓa taimaka musu da wani abu.
Ya ce, “Idan gwamnati ta shigo za mu ji daɗin haka. Tana da damar da za ta taimaki al’umma. Amma gazawar gwamnati ce ma ta sa su suka sadaukar da kansu da dukiyarsu domin amfanar al’umma don in ka tsaya ka ce sai gwamnati ta yi maka ba abin da za ka yi,” in ji shi.
Suna shirye duk wata ƙungiya ta cigaban al’umma da masu kishin sana’ar noma a shirye suke kowa su zauna da shi su yi tsari kamar yadda ɗaya daga manyan baƙi da ya halarci taron ba da horon Wazirin Hausawan Afirka, Ambasada Abubakar Usman Saraki ya yi na ɗaukar nauyin za a yi wa mutum 100 irin wannan horo. Don haka a shirye suke masu hali su shigo su ba da gudunmuwa wajen ɗaukar nauyin ba su irin wannan horo.
Ambasada Abba Hassan Baban Maja ya ce, “Ba kawai a jihar Kano ko sassan ƙasar nan ba ina zuwa ƙasashen Afirka inda Hausawa suke na yi musu irin wannan horo, ina ga maganar jihar Kano ko Arewa? Don haka a shirye muke, ƙofa a buɗe take ga duk wanda yake gani zai taimaka ya zo a yi haɗin gwiwa a taimaki musamman mata da matasa don bunƙasa tattalin arziƙin al’umma.”
Shi ma babban baƙo da ya halarci taron Wazirin Hausawan Afirka, Ambasada Abubakar Usman Saraki ya yaba wa Kungiyar bisa wannan tsari da ta kawo ganin zamani ya canza an dade da barin mu a baya ta bi gida-gida ta samo matasa maza da mata ta koya musu sana’a kuma ya ja hankalin mata kada su shiga gidan miji ba su iya sana ba saboda duniya ta sauya.
Ambasada Abubakar Usman Saraki ya taya waɗanda suka sami nasarar koyon sana’a murna da kira gare su su yi riƙo da sana’ar da aka koya musu da muhimmanci.