Tue. Apr 1st, 2025

Ƙungiyar Masu Gidaje A Kasuwar Kantin Kwari Ta Karrama Wasu Daga ‘Yan Ƙungiyar Masu Sassauta Kuɗin Haya

By Saleh Aliyu Feb 10, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa duk lokacin da abokan sana’a a rayuwa za su zaɓi wasu mutane su karrama su saboda gamsuwa da irin rawar da suke takawa domin yaba abin da suke ne da kuma zaburar da wasu yin koyi da su.

Shugaban ƙungiyar Kano Proper tsohon shugaban ƙaramar hukumar Fagge, Hon..Habib Saleh Mailemo ne ya bayyana hakan a taron karramawa da ƙungiyar masu gidaje na kasuwar Kantin Kwari ta yi wa wasu daga ‘yan ƙungiyar sakamakon gamsuwa da gudunmuwa da suke bayarwa.

Ya ce taro ne na haɗin kai da ya yi farin ciki da aka gayyace shi har aka ba shi dama ya miƙa shaidar karramawa ga wasu daga cikin ‘yan ƙungiyar saboda yabawa da abin da suka yi.

Habibu Mailemo ya ce ya kamata a ce dukkan sauran wasu da suke wata sana’a su cigaba da abubuwa irin wannan don zaburar da al’umma wajen yin aiki na alkhairi.

Alhaji Ƙasim Umar Warure da aka karrama a taron wanda Alhaji Muhammad Ƙasim Umar da ɗan’uwansa suka wakilta sun ce tun suna yara suke ji ana yi wa Alhaji Ƙasim Umar godiya kan alheransa har suka taso suka taras da abubuwa da ake yi suna yi wa Allah godiya da addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya.

Muhammad Ƙasim Umar ya ƙara da cewa wannan karramawa za ta ƙara musu ƙwarin gwiwa a kan yin aikin alheri kamar yadda addini ya nuna duk abin da aka yi na alheri zai bibiyi mutum har bayan rayuwa.

Alhaji Balarabe Tatari shi ne shugaban masu gidaje na kasuwar Kantin Kwari ya ce sun shirya taron ne saboda karrama wasu masu gidaje da suke sassautawa ‘yan kasuwa kuɗin haya saboda an shiga yanayi da wasu da yawa masu gidaje na ƙare-ƙaren kuɗi duk shekara.

Don haka suka ɗauki matakin duk wanda ya ƙara kuɗin haya su je wajensa su roƙi alfarma ya sassauta wa mutane sun je wasu sun yi alfarma har akwai wanda ya ce duk wanda yake cikin kantinsa ma zai sayar masa domin ya mallake shi sun yi nasara wasu sun ba su haɗin kai an rage.

Ambasada Balarabe Tatari ya ce sun yi wannan karramawa ne domin jan hankalin waɗanda ba su yi ƙarin kuɗi ba kar su yi domin a saukakawa al’umma, akwai wasu kamar gidan Alaramma da aka yi musu ƙorafi a kan halin da ake ciki sun yi ragi ne ma haka suke so masu gidaje su yi.

Ambasada Balarabe Tatari ya ce, aƙalla akwai sama da gidaje 270 a kasuwar Kantin Kwari da mutane sama da 30,000 ke kasuwanci a ciki, sannan akwai Kantuna da ba a gidaje suke ba, da kuma ɗaiɗaiku na gwamnati.

A yayin taron dai malamai daban-daban sun yi jawabai a kan maudu’ai da ya shafi harkar kasuwanci da tausayi da taimako.

An karrama mutane 22 a yayin taron da aka gudanar rufafffen ɗakin wasa na Sani Abacha a Kano.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *